1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata na shan kalubale saboda 'yan ta'adda

March 8, 2017

Yayin da mata a duniya ke bukukuwan ranar mata, a Najeriya mata na nuna bakin ciki kan yadda Kungiyar Boko Haram ke yin amfani da su wajen kai harin kunar bakin wake.

https://p.dw.com/p/2YqMT
Nigeria Flüchtlingskamp Yola
Hoto: Reuters/A. Sotunde

Ranar takwas ga watan Maris na kowace shekara rana ce Majalisar Dinkin Duniya ta ware domin yin biki ranar mata ta duniya domin yin nazari na ci gaba ko akasin haka da nufin tabbatar da cewa mata na samun hakkoki tare da ba su gurabe kamar yadda ake bai wa maza.

Taken bukin bana dai na fatar cimma shirin dorewar muradan karni zuwa shekara ta 2030. Sai dai yadda ake amfani da mata wajen kai hare-hare kunar bakin wake a Najeriya na zama barazana ga cimma wannan manufofi inda masu rajin kare hakkin mata ke ganin ya zama dole a dauki matakai na yaki da amfani da mata wajen yin ta'addanci.
Yayin da mata a duniya ke bukuwan ranar mata ta duniya a Najeriya mata na nuna bakin ciki yadda Kungiyar Boko Haram ke yin amfani da mata wasunsu ma masu kanann shekaru kamar tara zuwa goma domin kai harin kunar bakin wake.

Nigeria Selbstmordattentäter greifen Hilfs-Zentrum in Maiduguri an
Hoto: Getty Images/AFP/Stringer

Daga watan Afrilun shekara ta 2014 da kungiyar ta fara kai harin kunar bakin wake ta hanyar amfani da mace a Gombe zuwa farkon shekarar da mu ke ciki kimanin mata 123 suka kai harin kunar bakin wake a sassan Najeriya kamar yadda mujallar FDD mai rahotanni kan yake-yake ta ruwaito.

Asusun kula da Mata na Majalisar Dinkin Duniya wato UNWOMEN ya tabbatar da alkaluma makamantan haka kamar yadda Peter Mancha mataimakin daraktan asusun a Najeriya ke cewa.

Nigeria 21 Chibok-Mädchen
Hoto: Picture-Alliance/dpa/EPA/STR

Kungiyoyin mata na bayyana damuwa kan yadda ake amfani da mata wajen kai hare-haren kunar bakin wake, abin da suka alakanta da jahilci da talauci da ya yi katutu tsakanin mata da yara mata musamman a jihohin shiyyar Arewa maso Gabashin Najeriya. Yanzu haka dai akwai dubban mata da ake zargin Kungiyar Boko Haram ta kamesu ta na garkuwa da su ciki har da 'yan matan sekandaren Chibok sama da 200.