1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amnesty ta zargi Sojojin Najeriya da lalata

Abdul-raheem Hassan
May 24, 2018

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta kasa da kasa, ta bukaci hukunci kan sojoji da ake zargi da aikata fyade kan mata da kananan yara a sansanonin gudun hijira.

https://p.dw.com/p/2yDz6
Stephanie Sinclair - Gewinnerin des Anja Niedringhauspreis 2017
Hoto: IWMF/Stephanie Sinclair

Kungiyar ta ce ta samu shedu kan zargin da ke nuna dakarun na amfani da matan kamin basu abinci, Amnesty ta koka kan rashin daukar kwararan matakan hukunta wadan da ake zargi duk da tarin hujjoji da ke gaban hukumomi.Tun shekarar 2016 'yan sanda ke kokarin bankado irin ta'asar lalata da ake zargin sojojin na aikatawa a sansanonin 'yan gudun hijira, amma sojojin sun sha musanta zargin.Kungiyar Amnesty International a Najeriya, ta ce lokaci ya yi da shugaba Muhammadu Buhari zai cika alkawarin kare hakkin 'yan gudun hijira da rikicin Boko Haram ya raba da gidajensu.