1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata sun fara kama ko wacce sana'a

Ramatou Issa Wanke / LMJJune 29, 2016

A Jamhuriyar Nijar mata matasa ne suka mai da hankali ga aikin gyaran fanfo a wani mataki na dogaro da kai,wanda kuma tuni suka samu karbuwa daga al'umma.

https://p.dw.com/p/1JFvR
Kokarin gyaran fanfo domin samun tsabtataccen ruwan sha
Kokarin gyaran fanfo domin samun tsabtataccen ruwan shaHoto: PA/dpa

Ita dai Hajara Mamoudou mai kimanin shekaru 19 a duniya, ta bawa mutane da dama mamaki kasancewarta matashiya mai karancin shekaru wadda kuma ta shiga yin wannan aikin don raba kanta da zaman banza. To sai dai matsalar da mafi yawan mata masu aikin hannu ke fuskanta daga wasu mutane shi ne kyama da ma nuna cewa matan wannan aikin bai kamace su ba inji Harunnan Kimba shugaban masu gyaran fanfo.


Duk da irin kashedin da wasu mutanen ke yi ga Hajara da ma sauran matan da ke da niyar shiga wannan aikin da cewa aikin maza ne, hakan bai hanata bayyana irin ci-gaban da take ganin ta samu a cikin wannan aikin. Tuni dai wasu manazarta suka fara kira ga sauran mata da su yi koyi da Hajara domin suma su zamo masu dogaro da kansu.