Mata masu gyaran babur a jihar Maradi | Shiga | DW | 21.12.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Shiga

Mata masu gyaran babur a jihar Maradi

A garin Jiratawa na cikin Maradi ta Jamhuriyar Nijar, wasu mata ne suka rungumi sana’ar gyaran moto, a wani mataki na kawo sauyi a rayuwarsu da ta kasa baki daya

A birnin Maradi na Jamhuriyar Nijar wasu mata ne suka rungumi sana’ar gyaran moto, a wani mataki na kawo sauyi a rayuwarsu da ta kasa baki daya. Sana’ar gyaran moto ko babur sana’a ce wacce ga al'ada maza kadai ne ke yinta. To amma yanzu suma mata sun fara kirshe zanansu suna rungumar wannan sana’a dan samun dan abun biyan bukantunsu na yau da kullum. Malama Nana Badiya Adamu ,da Saudatu Issa matan da suka rungumi sana’ar aikin gyaran moto ko babur a garin Jiratawa karamar hukumar da ke cikin gundumar  Madarunfa ta jihar Maradi, kuma malama Saudatu Issa wacce matar aure ce, ta bayyana dalilan da suka sa ta rungumi wanan sana’a:


"Gaskiya dan na gani tana da anfani na rungumeta. Akwai cigaba na koya kuma na iya. Duk dai cikin harakar gyaran moto babu abin da ban iya ba, in na duba ina iya gane inda ya lalace. Ko wani ya kwance injin za ni iya gyara shi kuma in maida yadda yake. Gaskiya alhamdu lillahi na kware,kuma duka aikin da da namiji yake iya yi mata ma suna iya shi, sai wadda ta sa kissa a ciki.Saidai a gaskiya da farko na ji nauyi amma yanzu na murje idanuna babu wata kumya domin wanan aiki cigaba ne"


Ita kuma 'yan mata Nana Badiya Adamu mai kimanin shekara16 da ke zaman macce ta biyu a cikin mata masu gyaran babur, ta bayana jin dadinta da alfanon wanan sana’ar da suka runguma.


"Na ji dadi sosai da na rungumi wanan aiki na gyaran moto, dan gyaran moto yana da amfani da rihin asiri, ina iya gyra ko wane iri aka kawo mini, ina iya sa silanda, in gyra kapireto,in kwance birki , in gyara kuma in maida, ina tukawa dan jin ko gyara ya yi, idan bai yi ba sai na sake gyarawa. Ina amsar kudi amma ba kamar magyara maza ba, akwai amfani saboda ina gida sai a kawo mini moto in fito in gyara kuma in koma cikin gidana".


Adamu Musa magajin garin Jiratawa ne ya yaba da wanan kokari da wadanan mata suka yi:


" Wadanan mata gaskiya sun kware a panin gyara moto,ita mace in tana aiki ba ta ha’inci ciki, shi ya sa muka kira maza da mata su kawo gyaran baburansu wurin wadanan mata, hanya ce kyakyawa ta goge talauci, su dauki nauyin kansu, su dauki nauyin diyansu su taimaka ma mazansu, su taimakama al’uma duka".


 Wanan dai shi ne karo na farko da wasu mata na jihar Maradi suka rungumi sana’ar aikin gyaran moto ,sana’ar da a baya ake ganin maza kadai ne ke rungumarta, abin da ke nuna a fili cewa an fara samun sauyi a rayuwar matan Niger.