1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Mata masu dinkin hula jihar Jigawa

June 28, 2017

A yayin da Gwamnatin Tarayya Najeriya ke kokari na bunkasa harkokin kasuwanci a yankuna daban-daban na kasar, yanzu haka masu sanar dinkin hula a jihar Jigawa na bada himma sosai wajen sana'ar ta su.

https://p.dw.com/p/2fTUr
Nigeria Besticken traditioneller Kopfbedeckungen
'Yan mata masu dinkin Hulla a garin Gandu na jihar Jigawa a tarayyar NajeriyaHoto: DW/Z. Rabo Ringim

Garin Gandu ya na daya daga cikin kauyuka a jihar Jigawa da ke arewacin Tarayyar Najeriya, inda mata suka gwanance wajen dinkin hulla Zanna Bukar, inda ba su da wata sana'a da ta wuce dinkin hullar Zanna Bukar. Hajiya Marka Muhammad na daga cikin masu dinkin hukkar ta yi bayani kan dalillansu na yin dinka hular Zanna Bukar da kuma sauran hulluna:

"Ina zaune a garin gandu bakomai ne ya sa muke yin hula ba, zama kawai da rashin kwararan sana'o'i da kuma neman rufa wa kanmu asirin. Sabili da munajin dadin yadda da wannan dinkin hulla mu ke samun biyan wasu bukatunmu. Musali idan muka dinka daya ko guda biyu muka sayar, za ka samu kudin da za ka rufa wa kanka asiri."

A halin yanzu dai sana'ar dinkin hular ta fadada, inda kowane kauye ka zagaya za ka ga masu dinkin hulla, kuma nau'i na hullar Zanna Bukar su na da yawan gaske, musamman ma mata da kananan yara da ke wannan sana'a, sunyi kira ga gwamnati da ta san da zaman su, ta kuma sa mu su hannu na ganin an bunkasa sana'ar dinkin hullar da suke yi.