Masu zanga-zanga sun yi arangama da jami’an tsaro a ƙasar Chile, bayan mutuwar tsohon shugaban ƙasar Agusto Pinochet. | Labarai | DW | 11.12.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu zanga-zanga sun yi arangama da jami’an tsaro a ƙasar Chile, bayan mutuwar tsohon shugaban ƙasar Agusto Pinochet.

An yi wani mummunan ɗauki ba daɗi tsakanin jami’an tsaro da masu zanga-zanga a birnin Santiago na ƙasar Chile, bayan mutuwar tsohon shugaban ƙasar mai mulkin kama karya, Agusto Pinochet jiya lahadi. Wani kakakin ’yan sandan birnin ya fada wa maneman labarai cewa jami’an tsaro 23 ne suka ji rauni a arangamar, wadda ta ɓarke bayan da masu sukar lamirin gwamnati suka fara wata zanga-zanga ta nuna farin cikinsu ga mutuwar tsohon shugaban, gaban fadar gwamnati a birnin na Santiago de Chile.

Shugaban ƙasar mai ci yanzu, Michelle Bachelet ta ce ba za a yi wa Pinochet jana’izar girmamawa ta ƙasa ba, kuma ba za a keɓe wasu ranaku tamkar na juyayin mutuwarsa ba. Ita dai shugaba Bachelet da iyayenta, na cikin waɗanda Pinochen ya ɗaure a kurkuku a lokacin mulkinsa na mulkin kama karya a ƙasar. Alƙaluma dai na nuna cewa, fiye da mutane dubu 3 ne suka rasa rayukansu, ko kuma aka gallaza musu a gidajen yari, a tsawon shekaru 17 da Agusto Pinochet ya yi mulki a ƙasar Chilen. A gobe talata ne dai za a yi jana’izarsa a birnin Santiago, tare da bukuwan girmawa irin ta soji.