Masu zabe a Iraki sun amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar | Labarai | DW | 25.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu zabe a Iraki sun amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar

Hukumar zaben kasar Iraqi ta ce an amince da sabon kundin tsarin mulkin kasar na farko. Sakamakon karshe da ta bayar ya nunar da cewa kashi 78 cikin 100 na wadanda suka kada kuri´a a ranar 15 ga wannan wata sun jefa kuri´ar amincewa da kundin tsarain mulkin yayin kashi 21 cikin 100 suka yi watsi da shi. Yanzu haka dai tsarin mulkin ya zama doka bayan da masu adawa suka gaza samun rinjayen kashi biyu cikin uku na larduna 3 daga cikin 18 a fadin kasar baki daya. A ci-gaba da tashe tashen hankula a fadin kasar ta Iraqi kuma mutane 9 sun mutu sakamakon fashewar wani bam da aka dana cikin mota a birnin Sulaimaniya na ´yan Kurdawan arewacin Iraqin. Majiyoyin jami´an tsaro sun ce bam din ya fashe ne kusa da ginin jami´an gwamnatin yankin. A birnin Bagadaza kuma wani yaro ya rasu sannan mutane 9 sun jikata a fashewar bam a gefen hanya kusa da ayarin motocin dakarun Amirka. A jiya litinin akalla mutane 17 sun rigamu gidan gaskiya a fashewar bama-bamai 3 da aka auna akan wasu otel-otel da ake sauke ´yan jaridun kasashen ketare.