1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu yajin cin abinci a sansanin Guantanamo ya ninka sau biyu

Yawan firsinoni dake yajin cin abinci a sansanin sojin Amirka da ke Guantanamo a can Kuba, yanzu ya ninka zuwa mutum 84. Wani rahoto daga sansanin na Guantanamo ya tabbatar cewar a cikin wannan makon firsinoni musulmi guda 46 ne suka shiga jerin masu yajin cin abincin don nuna adawa da tsare su a sansanin. Lauyoyin su sun bayyana yajin cin abincin da cewa wata bijirewa ce da ta dace don nuna adawa da rashin kyawon yanayi a kurkuku da kuma hana su ´yancin daukar lauyoyin kansu.