1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masu neman sabbin wakilci a komitin Sulhu

Zainab A MohammadMay 17, 2005

Kasashen Jamus da India da Brazil da Japan na neman amincewa

https://p.dw.com/p/Bvbx
Hoto: AP

Kasashe hudu sun fara tattauna yiwuwan samun zaunannen kujeru a komitin sulhun mdd.

Kasashen Jamus da India da Japan da kuma Brazil sun gabatar da takardar neman doka dake kira ga fadada wakilcin komitin sulhun mdd daga 15 zuwa 25.Kasashen dai na bukatar a bawa sabbin wakilan dake neman shiga guda shida iko daidai dana wakilai biyar dake zaunannun kujera a komitin sulhun a halin yanzu,kana sauran hudun su kasance wakilai,kamar wakilai goma na yanzu.

Wannan takarda dai na nuni dacewa akwai bukatar fadada komitin sulhun domin kalubalantar yanayi na ainihi da duniya ke ciki.

Wannan bukatu na kasashen yazo ne yini guda bayan Amurka ta sanar da manufar tan a nuna adawa da fadada wakilcin komitin sulhun idan har sabbin shigan na bukatar zaunannun kujeru,wanda kuma na iya basu daman hawan kujeran naki kan kowane irin doka da komitin zata zartar.

A hannu guda kuma kasar Sin tayi gargadin cewa amincewa wannan wannan kuduri na bawa japan zaunannen kujera a komitin sulhu zai kawo barazana cikin harkokin gyare gyare na mdd.

Kakakin maaikatar harkokin waje na kasar Sin Kong Quan ya bayyana cewa har yanzu akwai gibi babba tsakanin wannan shirin doka da kuma kasashe da dama da suka hadar da Sin.Ya kara dacewa akasarin kasashen nada banbance banbance dangane da wannan shirin gyaran ,idan kuwa aka gabatar da wannan bukatu na sabbin wakilan dake neman shiga komitin sulhun zai ruruta wutan rikici.

Yayi fatan cewa kowace kasa dake neman shiga komitin zatayi nazari sosai tare da laakari da sauran wakilai da kuma ainihin makasudun mdd.

Tun a baya dai Sin ta fito karara tayi adawa da bawa Japan wannan kujera a komitin sulhun mdd,inda tace dole net a gyara kura kuran da take dashi na tarihin irin rawa da ta taka a yakin duniya.

A yanzu haka dai ana zagayawa da wannan shirin doka tsakanin wakilai da zasu iya daukan nauyin gabatar dashi a zauren taro na mdd a watan Satumba ,da kuma kungiyar kasashe dake goyon bayan yiwa mdd gyaran fuska.

Wadannan kasashe hudu dai zasu gabatar da wannan bukatu nasu a zauren mdd,idan sunyi imanin cewa kashi 2 daga cikin ukun wakilai 191 na mdd zasu mara musu baya.Takardar dai bata bayyana kasashen da zasu nemi zaunnannun kuran ba,sai dai tace biyu daga yankin Asia,da kasashe biyu daga nahiyar Afrika,da daya daga yammacin turai kana gudan kuma daga Latin Amurka.Ayayinda Afrika da Latin Amurka da Asia da gabashin Turai kowanensu zai samu wakilci.

Kasahen India,da Jamus da Japan da Brazil dai sunce kowane daga cikin sabbin wakilan ya samu yanci daidai da masu zaunnannun kujera da suka hadar da Britania,da Sin da Faransa da Rasha da kuma Amurka.