Masu gudanar bincike a Indonesia sun gano na´urar daukar magana jirgin saman da ya yi hadari | Labarai | DW | 07.03.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu gudanar bincike a Indonesia sun gano na´urar daukar magana jirgin saman da ya yi hadari

Masu binciken musabbabin aukuwar hadarin jirgin saman nan a Indonesia sun gano akwatin rikodar bayanai na jirgin saman da ya fadi lokacin da yake kokarin sauka a filin jirgin saman birnin Yogyakarta dake tsibirin Java. Har yanzu ba´a san musabbabin aukuwar hadarin ba, amma FM Australiya John Howard ya ce ba bu wata alama ta makarkashiya. Kamfanin jirgin saman wato Garuda Airlines ya ce fasinjoji 21 da mutum daya mai aiki a cikin jirgin sun rasu, amma da farko mai magana da yawon gwamnatin Indonesia ta ce mutane 49 suka rasu sakamakon hadarin. Wata tawagar jami´an diplomasiyar Australiya da ´yan jaridun kasar na cikin jirgin saman. Ministan harkokin wajen Australiya Alexanderb Downer ya ce har yanzu ba´a ga wasu ´yan kasar su biyar ba.