Masu garkuwa a Iraqi sun sake baiwa Jamus wani waadi game da bajamushiya da suka sace | Labarai | DW | 03.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu garkuwa a Iraqi sun sake baiwa Jamus wani waadi game da bajamushiya da suka sace

Kungiyar da tayi garkuwa da wata Bajamushiya da danta a kasar Iraqi sun sake baiwa gwamnatin jamus wani waadin kuma.

Cikin wata sanarwa da ta aike ta yanar gizo kungiyar tace zata kashe wannan mata da danta muddin dai Jamus bata janye dakarunta daga kasar Afghanistan cikin kanaki 10 ba

Cikin wani hoto na biduiyo matar Hanalore Krause yar shekaru 61 ta roki gwamnatin Jamus data biya bukatun wadannad sukayi garkuwar da ita.

Watanni 2 da suka shige ne aka sace wannan mata da danta a birnin Bagadaza.

Wannan kuma shine karo na biyu da masu garkuwar suka baiwa gwamnatin jamus din waadi na janye sojojinta daga Afghanistan ko kuma su kashe matar da danta.