Masu fashin jirgi sun mika kai a Turkiyya | Labarai | DW | 18.08.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu fashin jirgi sun mika kai a Turkiyya

Mutane biyun da suka yi fashin jirgin saman nan na Turkiya tuni sun mika kai hannun jami´an tsaro.An dai cafke mutane biyun ne bayan da jirgin ya sauka a garin Antalya ne. Matukan jirgin dai sun shaidawa yan fashin cewa akwai bukatar yada zango a Antalya din ne don karawa jirgin man fetur.Kafin saukar jirgin, masu fashin nasa sun bukaci saukar sa a birnin Tehran din kasar Iran ne.Yan fashin da suka ce su yan kungiyyar Alqeda ne, sun bukaci karkata akalar jirgin ne, jim kadan bayan tashin sa daga arewacin Cyprus izuwa birnin Istanbul. A dai lokacin da mutane biyun ke kokarin fashin jirgin akwai fasinjoji 136 a cikin sa. Tuni dai fasinjojin da kuma matukan jirgin suka samu yancin su, jim kadan da saukar jirgin a filin jirgin sama dake garin na Antalya.