Masu daukaka kara a Rwanda sun bukaci daurin rai da rai | Labarai | DW | 26.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu daukaka kara a Rwanda sun bukaci daurin rai da rai

Masu gabatar da ƙara a kotun Majalisar Dinkin Duniya kan laifukan yaƙi a Rwanda sun bukaci a yanke hukuncin ɗaurin rai da rai kan wani limamin Roman katolika na farko da yake fuskantar shari`a game da kisan kiyashi na Rwanda.A bara a ka yanke wa father Athanase Seromba ɗaurin shekaru 15 bisa zargin bada taimako da haɗin kai a kisan tutsi 800,000 da wasu yan Hutu na Rwanda fiye da shekaru 10 da suka shige.

Masu ɗaukaka ƙaran sunce hukuncin bai yi daidai da laifuka da ya aikata ba.An dai zarge shi ne da haɗa baki da hukumomin wajen rusa cocinsa inda mutane 1,500 suka nemi mafaka ciki.Dukkaninsu kuma sun rasa rayukansu .