Masu ciwon suga na ci-gaba da karuwa a duniya | Labarai | DW | 06.04.2016
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masu ciwon suga na ci-gaba da karuwa a duniya

Akalla mutane miliyan 422 ke fama da ciwon sugaa fadin duniya, abin da ke nunin cewar addadin ya ninka har sau hudu daga shekara ta 1980.

Da take magana a shafin farko na kundin rahoton, babbar darakta hukumar ta WHO Margaret Chan ta ce ciwon suga a halin yanzu ba wai ciwo ba ne na kashe masu karfin tattalin arziki ba, cuta ce da ke ci gaba da yaduwa a ko'ina cikin duniya. Hukumar ta ce wannan addadi da aka bayar na mutane miliyan 422 addadi ne ya zuwa shekarar 2014, inda a shekarar 1980 ake da mutane miliyan 108 masu dauke da cutar.

A shekarar 2012 dai ciwon suga ya yi sanadiyyar rasuwar mutane miliyan daya da rabi da kuma rasuwar wasu mutane miliyan biyu da dubu 200 a duniya sakamakon wasu cututtukan da ciwon sugan ke haddasawa. Mafi yawan masu wannan ciyon dai na a yankin Kudancin Asiya da Pacifique.