Masu canji kuɗaɗe a Najeriya na fuskantar matsaloli
February 5, 2016
Ba tun yau ba ne ake faɗi in faɗa tsakanin masana ilmin tattalin arzikin ƙasa da kuma jami'an gwamnati a game da yada za iya farfaɗo da darajar Naira wanda a yanzu haka ta faɗi a bisa kasuwani. A sabbin matakan da bankin ya ɗauka na baya-bayan nan shi ne dakatar da bai wa ƙungiyar 'yan canji kuɗaɗen dala sai dai su fantsama kasuwa su nema abin da hakan ya haifar da kace-nace .Shugabannin ƙungiyar dai a baya sun tabbatar da rashin aikin yi ga wasu ya'yan ƙungiyar sama da dubu 30 idan har wannan doka ta zauna daram a Najeriya .
Ya'yan ƙungiyar na 'yan caji sun faɗa cikin tasko
Alhaji Aminu Gwadabe shi ne shugaban ƙungiyar na ƙasa ya kuma tabbatar da cewar ya'yan ƙungiyar sun fada cikin tasku.''Zance gaskiyya kaso 80 cikin ɗari na ya'yan ƙungiyar ba su da wata sana'a bayan canjin kuɗaɗen inda ta haka ne za su shiga cikin taskun rayuwa.''A yanzu haka dai dalar Amurka ɗaya daidai take da aƙalla sama da Naira kusan ɗari uku wanda hakan ke nuni da cewar akwai jan aiki a gaban gwamnatin.
Yadda lamarin ya shafi kamfanoni canjin a Najeriya
A Najeriya dai aƙalla akwai kanfanonin 'yan canji sama da dubu biyu tare da ma'aikata sama da dubu ɗari biyu ke da akwai. Alhaji Gwadabe ya ce mafita ɗaya ce da za ta warware sarƙaƙƙiyar da suka shiga ciki .''Dole ne a buɗe hanyoyin yin muamalla da Western Union da gram da duk wata sabuwar hanya da kuɗaɗen ƙasashen ƙetare.'' Bincike ya nuna cewar gwamnatin Najeriya ta fara ɗaukar matakai domin farfaɗo da fannin tattalin arzikin ƙasar a duk faɗin ƙasar baki ɗaya.