MASU AZABTAD DA FURSUNONIN IRAQI A BAYAN SHINGE SUKE. | Siyasa | DW | 05.05.2004
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

MASU AZABTAD DA FURSUNONIN IRAQI A BAYAN SHINGE SUKE.

A halin yanzu dai, an gano cewa, ma’aikatan kamfanonin tsaro masu zaman kansu, na cikin wadanda suka fi azabtad da fursunonin Iraqi a gidan yarin Abu-Ghraib da ke birnin Bagadaza. Ana sanya alamun tambayoyi, a kan matakan da suke dauka na yi wa fursunonin tambayoyi. Har ila yau kuma, akwai dubannin irin wadannan jami’an, da kuma na kungiyar leken asirin CIA a Iraqin, wadanda ke cin karensu babu babbaka. Ko wane irin mataki mahukuntan birnin Washington ke niyyar dauka, don hana al’amura kara tabarbarewa a Iraqin ?

Yadda ake nuna wa fursunonin Iraqi azaba a gidan yarin Abu-Ghraib, a birnin Bagadaza.

Yadda ake nuna wa fursunonin Iraqi azaba a gidan yarin Abu-Ghraib, a birnin Bagadaza.

A bainar jama’a dai, babu wanda ya san yawan kamfanonin tsaro masu zaman kansu, da ke yi wa ma’aikatar tsaron Amirka aiki a Iraqi. Amma a kewayen ma’aikatar, wato Pentagon, da ke birnin Washington, akwai ofisoshin irin wadannan kamfanonin tarwatse a ko’ina. Su ne kuma suka sami kwangila daga Pentagon, ta yi wa fursunonin Iraqin tambayoyi.

A lardin Arlington da ke jihar Virginia a can Amirkan, akwai daya daga cikin wadannan kamfanonin tsaron, mai suna CACI. Kamar dai wasu kamfanoni irinsa, ofishin CACI din na kusa-kusa ne da ma’aikatar tsaron ta Pentagon. A shafin Internet ma, kamfanin na sanya tallar neman ma’aikata, wadanda za su dinga gudanad da tamabyoyin da suka shafi harkokin tsaro. Duk da cewa, kamfanonin na samun kwangilarsu ne daga Hukumar rundunar sojin Amirka, amma ba sa bin ka’idojin sojin, ko kuma dokokin kasa ta Amirkan wajen gudanad da ayyukansu. Kamar yadda Robert Baer, wani tsohon ma’aikacin kungiyar leken asirin CIA ya bayyanar:-

"Wadannan mutanen, ba sa ganin wani nauyi ya rataya a wuyarsu. Ba sa bin dokokin Amirka ko kuma na Iraqin."

Kungiyoyin kare hakkin dan Adam da dama na zaton cewa, sabili da hakan ne, ma’aikatar tsaron Pentagon ta fi dogara kan ire-iren wadannan kamfanonin, wajen samad da jami’an da take turawa ketare, a abin da take kira "yaki da ta’addanci". A ganin Douglas Brook, na rukunin kungiyoyin fafutukar samad da zaman lafiyar nan "International Peace Organisations":-

"A galibi, tsoffin sojojin Amirka ne wadannan kamfanonin ke turawa zuwa yin tambayoyin, wato sojojin da suka yi kimanin shekaru 10 zuwa 15 kafin su bar aiki. Idan sun fara pansho ne, ma’aikatar Pentagon din ke neman irinsu, don ba su kwangilar gudanad da wadannan ayyukan. Amma da zai dai fi dacewa, idan aka shimfida wa wadannan mutanen sharuddan gudanad da aikinsu karkashin dokokin soji."

Amma a zahiri, ba haka lamarin yake ba. Suna aikinsu ne, kamar sauran jami’an leken asiri, a bayan shinge. Bisa ka’ida dai, `yan sandan soji ne ke dauke da nauyin kula ko kuma yi wa fursunonin yaki tambayoyi. Amma Janis Karpinski, wani tsohon shugaban `yan sandan sojin Amirkan a Iraqi, wadanda yanzu ake tuhumarsu da nuna wa fursunonin na gidan yarin Abu-Ghraib azaba, ya bayyana cewa:-

"Na tabbatar cewa, ba haka kawai jami’an da ke karkashina suka tashi suka dinga azabtad da fursunonin ba. Sanin kowa ne cewa, jami’an leken asirin da aka ba su kwangilar gudanad da tambayoyi ne suka ba su umarnin daukan wasu matakan da ba su dace ba. Su ne suka umarce su su bar fitillun dakunan sarkan a kunne, ba dare ba rana, da dai makamncin haka."

Kamfanin CACI din dai ya ce, kawo yanzu babu ko daya daga cikin ma’aikatansa, wanda aka samu da wani laifin da ake zargin jami’an tsaro a Iraqin da shi.

Sakatren tsaron Amirkan, Donald Rumsfeld dai, ya ba da sanarwar cewa, za a gudanad da bincike kan duk kararrakin da aka bayyana su yanzu da kuma irin hanyoyin da ake bi na yi wa fursunonin tambayoyi, a duk gidajen yarin sojin Amirkan, a cikinsu nkuwa, har da sansanin nan na Guantanamo. Majalisar datttijan Amirkan kuma, ta ce za ta gudanad da bincike kan wannan batun. Ta hakan ne dai , watakila, za a iya tsara wasu ka’idoji, wadanda za su shimfida yadda za a dinga yi wa fursunoninn yakin da ke hannun sojin Amirka tambayoyi da kuma bincike nan gaba.

 • Kwanan wata 05.05.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvjy
 • Kwanan wata 05.05.2004
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bvjy