Masu aikin agaji na gamuwa da cikas a ƙasar China
August 12, 2010Ayyuka agaji na ceto jama'a da zaɓtarwa ƙasa ta rutsa da su a ƙasar China sakamakon ambaliya ruwan da aka samu na gamuwa da cikas dangane da wani ƙarin ruwan samar kamar da bakin ƙwarya da aka sheƙa a daran jiya larba.
Mutane dai sama da dubu guda ne suka mutu a yankin arewa maso yammacin ƙasar yayin da 1700 suka yi ɓatan dabo a sanadiyar zaɓtarewar ƙasa da aka samu dakuma zubar laka a wasu yankunan dake kan tsauni.
kamfanin dilacin labarai na ƙasar Faransa AFP, ya ambato wani mai aikin agajin Han Huiping na ƙasar ta China ya na mai cewa kusan awowi fudu da aka ƙwashe a jiya ana tabka ruwan saman
ya sa hanyoyin sun sake datsewa, abinda kuma ya ce ya kawomasu cikas ga aikin rabon ruwan sha na pompi da kuma cimaka da suke yi ga jama'a
Mawallafi: Abdourahamane Hassane
Edita : Zainab Mohammed abubakar