Masifar girgizar kasa a yankin Kashmir a Pakistan | Labarai | DW | 21.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masifar girgizar kasa a yankin Kashmir a Pakistan

Mayakin Yan tawaye.

Mayakin Yan tawaye.

MDD ta sake yin kira da a kai daukin gaggawa ga jama´a da suka tagayyara a yankunan dake fama da masifar girgizar kasa na Pakistan. A lokacin day ake magana a birnin Geneva, babban jami´in dake kula da aikin jin kai na MDD Jan Egeland ya ce kawo yanzu an tabbatar da mutuwar mutane dubu 48 to amma yawan su ka iya ninka haka har sau biyu idan ba´a kai taimakon gaggawa ba. Egeland yayi kira da kungiyar tsaro ta NATO da ta fara kai dauki ta sama don raba kayan abinci da sauran kayakin da ake bukata ruwa a jallo ga dubun dubatan mutane da suka tsira daga wannan bala´i da ya addabi yankin Kashmir. Da farko dai shi ma babban sakataren MDD Kofi Annan ya yi kira ga kasashen duniya da su kara yawan taimakon da suke ba Pakistan don hana abin da ya kira mace macen dubban mutane musamman yanzu da sanyin hunturu ke karatowa.