1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masifar ambaliyar ruwa a Nijar

August 29, 2010

A jamhuriyar Nijar kimanin mutane dubu ɗari biyu suka rasa gidajensu, sakamakon ambaliyar ruwa

https://p.dw.com/p/OyuD
Gadar Kennedy dake bisa kogin Isa, kusa da NyamaiHoto: picture-alliance/ ZB

Wasu alƙaluman da Majalisar Ɗinkin Duniya ta fitar, sun bayyana cewa kimanin mutane dubu ɗari biyune suka rasa gidajensu a Jamhuriyar Nijar sakamakon ambaliyar ruwa. Majalisar tace a ƙasar Nijar wanda ta yi fama da ƙarancin abinci yanzu ambaliyar ya tafi da gidaje kimanin dubu talatin. Wannan adadin ya ruɓɓanya alƙaluman da aka bayar kwana biyar da suka gabata. Ƙungiyoyin bada agaji sukace lamarin wani babban tashin hankaline ga jamhuriyar ta Nijar, inda dama can mutane basu farfado daga raɗaɗin tamuwa ba, kuma wannan ambaliyar ruwan ta share gonakin da ake jiran su nuna a girbe. Ƙungiyar bada agaji ta OCHA tace yanzu haka ana buƙatar agajin abinci na ton dubu goma da borguna aƙalla dubu sittin, dama rigan sauro kamar dubu 34. Yanzu Majalisar Ɗinkin Duniya tace rabin yan ƙasar Nijar za su shiga mayuwacin halin na ƙarancin cimaka, idan dai duniya bata kawo ɗauki ba.

Mawallafi: Usman Shehu Usman

Edita: Ahmadu Tijjani Lawal