Masar ta yi gyaran kundin tsarin mulki
March 20, 2007Majalisar dokokin Masar ta amince da gyare gyare a wasu dokoki masu sarkakiya na kundin tsarin mulkin ƙasar, wanda yan adawa suka ce babbar koma baya ce ga dimokradiya a ƙasar ta gabas ta tsakiya. Shugaban ƙasar Hosni Mubarak ya gabatar da yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin a wani mataki da ya ce na haɓaka tafarkin dimokradiya a ƙasar wadda ya shafe shekaru 25 yana shugabancin ta. A hannu guda yan adawa sun ce gyagyaren kundin tsarin mulkin ya yi tarnaki ga bangaren shariá na sa ido a kan zaɓe wanda suka ce hakan ne kawai zai kare yin maguɗin kuriú. Bugu da ƙari sabbin dokokin sun baiwa shugaban ƙasar ƙarin ƙarfin iko a kan harkokin tsaro. Kakakin ƙungiyar Muslim Brothers babbar jamíyar adawa a majalisar dokokin ta zargi gwamnatin da zartar da dokoki na kama karya.