1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar ta shirya mayarda yan gudun hijira na Sudan gida

January 3, 2006
https://p.dw.com/p/BvDr

Kasar Masar ta shirya sake mayarda wasu yan gudun hijira na Sudan su 645 gida,sabanin rahotanni da aka baiwa MDD a yau talata.

Fatma Zahra Etman,mai magana da yawun maaikatar harkokin wajen Masar tace a ranar alhamis din nan zaa kori yan gudun hijirar zuwa gida ta karamin jirgin ruwa daga Masar.

Hukumar kula da yan gudun hijira ta MDD tun farko tace, ta samu tabbaci daga kasar Masar cewa, ba zata mayarda yan gudun hijira na Sudan gida ba,duk da rahotanni da kafofin yada labarai suke bayarwa sabanin hakan.

Kakakin hukumar Astrid van Genderen Stort ya fadawa taron manema labarai cewa babu wani rahoto da suka samu na tilastawa yan kasar ta Sudan komawa gida.

A yau ne wata jaridar kasar masar ta fito da labarin cewa,akwai wasu yan gudun hijira na Sudan da baa san yawansu ba,da ake tsare da su a wani sansanin soji kusa da filin jirgin saman birnin Alqahira da ake shirin mayarda su gida cikin kwanaki 2.

A ranar jumaa data gabata ne yan sandan Masar suka yi anfani da kulake da bindigogin ruwa domin korar yan gudun hijirar kusan su 3,500 da suke zanga zanga a wajen ofishin MDD inda mutane 27 suka rasa rayukansu.