1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar: al-Sisi ya yi kwaskwarima a majalisar ministocinsa

Yusuf BalaMarch 23, 2016

Kwararre a fannin aikin banki Amr el-Garhy an nada shi a matsayin ministan kudi na kasar, yayin da Dalia Khorshid an nada ta ministar harkokin zuba jari.

https://p.dw.com/p/1IIEC
Ägypten Präsident Al-Sisi
Shugaba al-SisiHoto: imago/Xinhua

Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-Sisi ya yi kwaskwarima ga majalisar Ministocinsa a ranar Laraban nan inda ya nada sabbin ministoci 10 ciki kuwa har da ministan kudi da zuba jari kamar yadda kafar talabijin a kasar ta Masar ta bayyana.

Kwararre a fannin aikin banki Amr el-Garhy an nada shi a matsayin ministan kudi na kasar, yayin da Dalia Khorshid kwararriya da ta taba aiki a kamfanin gine-gine na Orascom da aka bata mukamin ministar harkokin zuba jari.

Sauran mukaman da shugaba al-Sisi ya bayar sun hada da ministoci a ma'aikatun shari'a da na harkokin yawon bude ido da al'adu da harkokin aikin gwamnati da aiyyukan noman rani da sufurin jiragen sama da na kasa.