Masar na tuhumar wani mutun da laifin leken asiri | Labarai | DW | 17.04.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Masar na tuhumar wani mutun da laifin leken asiri

Hukumomin Masar suna tuhuman wani masannin ma’aikacin makamashin nukiliya da laifin yiwa Israila lekan asiri, tare da wasu abonkan aikin sa biyu daga kasashen Irish da Japan. Wani alkalin kotu da ya yi hira da manema labarai a birnin Alkahira, yace Mohammed Sayed Saber Ali, mai shekaru 35 da haifuwa, ya sace wasu muhinmman takardu daga hukumar makamashin nukiliyar kasar da niyar kaiwa wata kungiyar asiri ta Israila.