1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Salah zai je neman magani a Spain

Gazali Abdou Tasawa
May 28, 2018

Hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta Masar ta sanar da cewa shahararren dan wasan kwallon kafar kasar Masar Mohamed Salah zai je kasar Spain domin jinyar rauni da ya ji a kafada.

https://p.dw.com/p/2yTvn
Champions League Final - Real Madrid v Liverpool - Verletzung Salah
Hoto: Reuters/K. Pfaffenbach

Hukumar kula da wasannin kwallon kafa ta kasar Masar ta sanar a wannan Litinin da cewa shahararren dan wasan kwallon kafar nan na kasar Masar Mohamed Salah zai je kasar Spain domin jinyar rauni da ya ji a kafada a wasan karshe na cin kofin zakarun Turai.

Hukumar ta ce likitocin kungiyarsa ta Liverpool da na kasar ta Masar za su kasance a tare da shi a tsawon lokacin zaman jinyar tasa a Spain, ko da shike ya zuwa yanzu kungiyar tasa ba ta ce uffan ba kan wannan batu. Wasu kafofin yada labaran kasar ta Masar dai sun ruwaito wasu kwararrun likitoci na kasar na cewa ala kulli halin rauni da dan wasan ya ji zai dauki makonni uku kafin ya warke.

Sai dai a wani sako da ya aika wa magoya bayansa a shafinsa na Twitter a jiya Lahadi, Mohamed Salah mai shekaru 25 ya yi kiran da su kwantar da hankalinsu domin ya na kyautata zaton warkewa cikin kankanin lokaci da samun damar taka wa kasar tasa leda a gasar cin kofin kwallon kafa na duniya da za a soma a kasar Rasha nan da kwanaki 23.