1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Masar: Jana'iza da zaman makoki bayan hare-hare

Mahmud Yaya Azare
April 10, 2017

A yayin da al'ummar Masar ke zaman makoki da jimamin asarar rayukan da aka yi a majami'un Kibdawa, sakamakon tagwayen hare-haren, ana ci gaba da samun ra'ayi mabambanta tsakanin yan kasar.

https://p.dw.com/p/2b0gu
Ägypten Trauernde vor der koptischen Kirche Saint Mina in Alexandria
Dumbin jama'a sun fito domin jana'izar wadanda suka rasu a harin ta'addanci a MasarHoto: Reuters/A. Abdallah Dalsh

Har-haren da suka kai ga halaka kimanin kibdawa 60, da ke zama mafi muni a 'yan shekarun nan a tarihin ta'addanci kan wuraren ibada a kasar ta Masar, sun janyo kafa dokar ta baci tare da kafa wani kwamatin kar-ta-kwana don tunkarar ta'addanci da matsanancin ra'ayi.

Sai dai hakan ya janyo dasa ayar tambaya kan irin mahimmanci  da gatar da tsirarun Kibdawan ke dashi a kasar ta Masar. Kasashen Yamma dai na daukar Kibdawan kasar a matsayin tsirarun kuma 'yan lelen da ke shan tsangwama a kasarsu, sai dai irin gazawar da gwamnati ke yi wajen basu tsaron da ya wajaba, ya tabbatar musu da cewa, babu abun da zai fitar musu da kitse daga wuta, fiye da sajewarsu da sauran 'yan kasa, bisa tushen daidaito da adalci a cewar Imad Shafiee, kwararre kan halin zamantakewa a cibiyar bincike ta Al-Ahram :

Mabiya darikar Koptk a Masar na zaman makoki

Ägypten Beisetzung Anschlag in Alexandria
Mabiya darikar Koptik na Masar na nuna juyayiHoto: picture-alliance/AP Photo/S. Abdallah

 "Gwamnatin da ba za ta iya bai wa mutane kariya ba hatta a wajen ibadunsu, ba ta yadda za ta iya basu cikakkun hakkokinsu na 'yan kasa, wadanda suka hada da cikakken tsaro, more rayuwa, 'yanci da tabbatar musu da burace-buracensu na siyasa. Sakamakon mayar da Kibdawa 'yan lelen gwamnati a Masar. Yan ta'adda na daukarsu a matsayin bishiyar kuka mai dadin hawa,  don haka suke kai musu hare-haren ramuwar gayya, a yayin da su kansu kibdawan a gefe guda, suke zargin ana mayar da su saniyar ware. Dole ne mu fito mu fadawa juna gaskiya, domin muddin wanda aka cuta bai koka ba, to mai cutar zai ci gaba da yin cutarsa ne.”

Ägypten Trauernde vor der koptischen Kirche Saint Mark in Alexandria
Jana'izar 'yan darikar Koptik a AlexandriyyaHoto: Getty Images/AFP/M. El-Shahed

Jana'izar wadanda suka mutu a harin

 Su kuwa Mazauna yankin Sinai, yankin da ake kaiwa sojojin na Masar harin rokoki daga cikinsa, har ya sanyasa Isra'ila ta bai wa 'yan kasarta umarnin dakatar da kai ziyara a yankin da yahudawa suka saba kai wa ziyara da ma kasar ta Masar baki daya. Mahakumatan kasar ta Masar dai na zargin mazauna yankin na Sinai da bai wa mayakan sa kai na Ansaru  Baitil Maqdis da ke da alaka da kungiyar IS kariya a yankunan nasu, wadanda kuma dakarun sojin kasar sukace, sun halaka kimanin mutane dubu biyar a yankin, da rusa kimanin gidaje dubu talatin da ake amfani dasu wajen fasa kwabri zuwa yankin Gaza. Ko minene mafita, ga wannan matsala ta tsaro da siyasa a kasar ta Masar? Muhammad Al'amin, Editan jaridar Aljumhuriyyah ya bayyana ra'ayinsa:

Jami'an tsaro sun ja daga a harabar Mujama'u

Ägypten Polizist vor der koptischen Kirche in Tanta
Hoto: Reuters/M. Abd El Ghany

"Ya zama wajibi ga gwamnati ta nemi sasantawa tsakanin 'yan kasa, bisa tushen daidaito da adalci da kishin kasa. Hatta su kansu masu ra'ayin Islaman da ake tsare dasu da 'yan ta'addan da suka tuba, wajibi ne a basu dammar zama 'yan kasa na gari, ta hanyar basu dammar sajewa da jama'a da damar kafa kungiyoyi masu zaman kansu da na siyasa bisa akidar kishi da yi wa kasa hidima.”