1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Bam kusa da ofishin jami'an leken asiri a Masar

Yusuf BalaAugust 20, 2015

Wannan hari na bam dai na zuwa ne kwana daya bayan da shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya rattaba hannu kan wata sabuwar dokar yaki da ta'addanci.

https://p.dw.com/p/1GI8T
Ägypten Bombenanschlag in Kairo
Wurin da aka kai hari a MasarHoto: Reuters/M.A. El Ghany

Wani abin fashewa mai karfin gaske cikin mota ya tashi a kusa da ginin jami'an lekan asiri a Shubra da ke kusa da birinin Alkhahira fadar gwamnatin kasar Masar.

A kalla mutane shida ne suka sami raunika ciki kuwa harda dan sanda guda . Babu dai wasu rahotanni na wadanda suka rasa rayukansu ya zuwa yanzu a wannan hari da ya nufi ginin gwamnati da tuni glasan da ke a ginin suka tarwatse baje a kan titi.

Wannan hari na bam dai na zuwa ne kwana daya bayan da shugaba Abdel Fattah al-Sisi ya rattaba hannu kan wata sabuwar dokar yaki da ta addanci, wacce ake ganin ta kara wa 'yan sanda karfin iko da takure hakkokin al'umma da fadin albarkacin baki.

Wani da ake kira Muhammad Osama mazaunin yankin ya bayyana yadda yaga afkuwar lamarin.

Ya ce "Maharan da fari sun tsaya cikin motoci a danja, bayan da na'urar da ke bada hannu ta nuna alamar jan launi sai wasu mutane biyu suka rugo a guje suka shiga motar suka nufi ginin, mintuna uku baya, bam din ya tashi".

Babu dai wata kungiya da ta dauki alhakin kai wannan hari.