Marubuta sun zargi Turai da Afrika kan rikicin Zimbabwe da Darfur | Labarai | DW | 04.12.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Marubuta sun zargi Turai da Afrika kan rikicin Zimbabwe da Darfur

Wata ƙungiyar marubuta ta zargi shugabannin Turai da na Afrika da laifin nuna tsoro na siyasa saboda sun gagara sanya batun rikicin kasar Zimbabwe da na Darfur kan gaba cikin ajandar taronsu na ƙarshen mako da zai gudana a Lisbon.Marubutan waɗanda suka haɗa da Vaclav Havel,Ben Okri da kuma Gunter Grass wanda ya samu lambar yabo ta zaman lafiya sun zargi manyan yan siyasa da kaucewa daga manyan matsaloli biyu da yan adam ke fuskanta a duniya.Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe yace zai halarci taron tsakanin Ƙungiyar Taraiyar Turai da ƙasashen Afrika wadda kuma yin hakan ya tunzura Firaministan Burtaniya soke halartar taron.A halin da ake ciki kuma Amurka ta sanar da cewa zata kafa takunkumin zirga zirga da na karya tattalin arziki kan wasu jami`an da ke da alaƙa da Mugabe su 40,wanda hakan zai kai adadin waɗanda aka lakabawa takunkumin zuwa mutum 170. Amurkan tace shekarar 2007 itace shekara mafi muni ga batun take hakkin bil adama a Zimbabwe.