1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Marubucin waka Leonard Cohen ya mutu

Marubucin adabi kuma fitaccen mawaki ya mutu a shekaru 82, bayan gabatar da kundin wakokinsa na 14.

Fitaccen mawaki kuma marubucin adabi Leonard Cohen ya mutu a shekaru 82. Sanarwar da aka gabatar ta dandalinsa na sada zumunta, na bayyana mutuwar tasa a matsayin babban rashi a fannin harkokin shakatawa.

Sanarwat ta kara da cewar, za'ayi shirye-shiryen bizinarsa a birnin Los Angeles na Amurka. A watan Oktoban da ya gabata ne dai mawakin, wanda dan asalin kasar Canada ne, ya gabatar da kundin wakokinsa na 14.