1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin 'Yan Afrika ta yamma kan shari'ar Taylor

Zainab MohammedApril 27, 2012

26 ga watan Afrilun 2012, zata kasance a tarihi, dan gane da samun tsohon shugaban Liberiya Charles Taylor da kotun birnin Haag ta yi, da hannu a yaƙin basasar Saliyo da ya haddasa asarar rayukar dubban mutane.

https://p.dw.com/p/14mDv
People hold signs outside the Special Court for Sierra Leone, where people gathered to watch a live broadcast of the verdict in the Netherlands-based trial of former Liberian president Charles Taylor, in Freetown, Sierra Leone Thursday, April 26, 2012. Thousands of people who survived Sierra Leone's brutal civil war a decade ago celebrated Thursday after learning that Taylor had been convicted for his role in the conflict that left behind countless amputees and traumatized former child soldiers. (Foto:Felicity Thompson/AP/dapd).
Hoto: AP

Moussa na fidda hawaye. Yana tsaye ne a kofar shiga harabar kotu ta musamman da MDD ta kafa domin shari'ar masu laifukan yaƙin da aka tabka a Saliyo, dake birnin Freetown, inda ya kuma ya tsaya shiru yana tunani. Ɗaruruwan 'yan kallo nedai suka kalli lokacin da Alkalin kotun hukunta masu manyan laifuka da ke birnin Hague yake cewar, an samu tsohon shugaban Liberiyan da laifukan yaƙi 11, da suka hadar da kisan gilla, fyaɗe, nakasa wasu da tilastawa yara ɗaukar makamai domin yaƙi. Amma tunanin Moussa na musamman ne akan Iyayensa, da 'yan uwansa guda huɗu. Dukkansu dai 'yan tawaye ne suka hallakasu da bakin bindiga. Makaman da kotun Hague ta tabbatar da cewar Chrles Taylor sayar dasu ya karbi lu'u-lu'u.

"Cikin kuka Moussa yace...an kwatanta adalci ayau, ba wai ga mutanen Saliyo kaɗai ba amma g Afirka baki ɗaya, saboda wannan sako ne zuwa ga dukkan 'yan siyasa da mutanen da ke tunanin cewar zasu ci zarafin talakawa domin azurta kawunansu. Domin abunda Charles Taylor yayi kenan domin azurta kanshi".

A gefen Moussa kuwa, Jussu Jarka ne yake tsaye kana ganin idanunsa cike da kwalla, hannayensa duka biyu na karafa ne dake sarkafe daga kafaɗarsa. A hannunsa na dama yana rike da hankaci da yake share hawayensa. Jussu dai yana cikin wadan da 'yan tawayen suka gutsuttsure wa hannu, lokacin da suka kai hari a birnin Freetown a shekara ta 1999. Tun daga lokacin ya kasance wakilin ɗumbin mutanen da ke rayuwa da irin wannan nakasa sakamakon aika-aikan 'yan tawayen na Saliyo...

Ya ce " ina cike da farin ciki dangane da wannan hukunci da kotu ta yanke. domin mun jima muna jiran wannan shari'a. don haka ne muna cike da farin cikin ganin cewar an samu Charles Taylor da waɗannan laifuffukan da aka aikata akan al'ummar Saliyo".

Former Liberian President Charles Taylor (rear L) sits next to a security guard as he waits for the start of a hearing to receive a verdict in a court room of the Special Court for Sierra Leone in Leidschendam, near The Hague, April 26, 2012. A special court delivers its verdict on Thursday on whether Taylor is guilty of crimes against humanity by supporting and directing rebels who pillaged, raped and murdered during the Sierra Leone civil war. The verdict will be the first passed on a former head of state by The Hague's international courts in what human rights advocates say is a reminder that even the most powerful do not enjoy impunity. REUTERS/Peter Dejong/Pool (NETHERLANDS - Tags: CRIME LAW POLITICS)
Lokacin shari'arHoto: Reuters

Ana zaman ɗarɗar a Liberiya

A kasar Liberiya dake makwabtaka kuwa, martanin al'ummomin ya sha banban da na Saliyo, kasancewar ta kasarsa ta haihuwa, Charles Taylor yana da ɗumbin magoya baya. Saboda tsoron ɓarkewan rikici, Sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Ɗunkin duniya ne ke ci gaba da sintiri a titunan babban birnin kasar dake Monrovia, ayayinda ake ci gaba da gudanar da tsauraran bincike a filin saukan jiragen sama. Saɓani murna da al'ummar Saliyo ke yi, da yawa daga cikin 'yan Liberiya na ganin cewar tsohon shugaban nasu bashi da laifi, kuma kamata yayi kotu ta wanke shi.

Atmo......

Sandoh Johnson dake zama wani na kusa da iyalan Taylor ya zargi hukuncin da aka yanke masa da kasancewa rashin adalci da makarkashiyar kasashen yammaci na turai...

Ya ce " da yake yanzu Amurkawa da Britaniya sun cimma burinsu, ina ganin kasashen na ci gaba da yin makarkashiyarsu akan Liberiya. amma a nawa ra'ayin kamar yadda 'yan Liberiya masu yawa suka yi imani, Charles Taylor bai aikata wadannan laifuffuka da aka tabbatar akansa ba. domin mun san tsohon shugaban kasarmu, musan darajarsa, mutuncinsa, mun kuma sana abubuwan da zai iya aikata wa da waɗanda ba zai iya ba. Sai dai ba zamu bar wannan batu haka ba, zamu daukaka wannan kara har sai munga abunda ya ture wa buzu naɗi".

A yanzu haka dai akwai tada jijiyar wuya a Liberia , dalili kenan daya sa aka kaurara da shari'ar daga yankin Afrika ta yamma zuwa birnin Hague. Sai dai akwai 'yan Liberiya dake ci gaba da tausawa al'ummar ta Saliyo.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar

Edita : Umaru Aliyu