1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin shugabannin Ɗuniya akan sake zaɓen Barroso

September 16, 2009

Jose Manuel Barroso na cigaba da karɓan sakonnin taya murna

https://p.dw.com/p/JiL1
Jose Manuel BarrosoHoto: AP

Shugabannin ƙasashen Duniya da Jami'ai na cigaba da aikewa da sakonninsu na taya murna, wa shugaban hukumar gudanarwan na Tarayyar Turai, Jose Manuel Barosso bayan nasara daya samu a zaɓen daya gudana a yau laraba, wanda ke nufin karin wasu shekaru biyar akan madafan iko.

Priministan Britaniya Gordon Brown ya bayyana sake zaɓen Manuel Barroso domin shugabantar hukumar, matsayin babbar nasara a ɓangaren turai. Ya ce, na jima da nunar da cewar Barroso shine mutumin daya cancanci wannan matsayi. Brown yace ko shakka babu , akarkashin jagorancinsa , hukumar turai dama Turai baki ɗaya , zata cigaba da takalal batutuwa da suka shafi membobinta, da suka haɗar da samarda ayyuka, talauci, da kalubale kan harkokin tsaro da duniya ke fuskanta da kuma matsalar sauyin yanayi.

A ɓangarensa, shugaban Faransa Nicolas Sarkozy cewa yayi yana fatan ganin ingantuwan dangantakar haɗain kai da Barroso.Ya ce nayi matukar farin cikin ganin cewar, an sake bamu wata damar daɗa inganta haɗin kanmu, na cigaba da aikin da muka fara tun lokacin da Faransa take rike da zagayen shugabancin ƙungiyar Tarayyar Turai, wanda ya kunshi faɗaɗa ayyukan turai a dangane da matsalolin tattali dake da alaka da ƙalubale na Duniya baki ɗaya. Sai dai ya bukaci Barroso daya gabatar da ainihin ayyukan da hukumarsa zata tafiyar a na tsawon shekaru biyar masu gabatowa.

Jose Manuel Barroso und Jerzy Buzek
Barroso da Jerzy BuzekHoto: AP

Shi kuwa shugaban ɓangaren jam'iyyar masu kare muhalli a majalisa Daniel Cohn-Bendit, bayyana Barroso yayi da kasance kore shar kuma mai sassaucin ra'ayi...

" Ya ce babu mutum irinsa, babu mai sassaucin ra'ayi irinsa. Shine mutumin daya cancanci wannan matsayi, da zai haɗa kawunan mutane baki ɗaya"

Kazalika itama shugabar jami'iyyar adawa masu ra'ayin 'yan mazan jiya Manuela Ferreiro, bayyana wannan zaɓen tayi da kasancewa babban abun alfahari a ɓangaren ɗan majalisar na Portugal ɗin, kuma ɗan jami'iyyarta .

Ta ce irin nasarori daya samu a shekaru biyar da suka gabata ne , ya sake karfafa matsayinsa a hukumar Tarayyar Turan. Jose Manuel Barroso wanda ke kasancewa ɗan jami'iyyar Ferreira Leiter masu sassaucin ra'ayi na PSD, ya kasance priministan Portugal daga shekarata 2002 zuwa 2004, ya kasa ɓoye farin cikinsa dangane da wannan dama da aka sake bashi na jagorantar hukumar gudanarwan turan na karin shekaru biyar...

"Yace zuwa ga dukkan wakilan wannan majali...nayi niyyan aiki da dukkanninku a shekaru biyar masu gabatowa, domin mu samu sukunin gina kakkarfar majalisar turai mai demokraɗiyya"

Barroso ya kara dacewar a matsayinsa na shugaban hukumar, jammi'iyyarsa ita ce Turai,kuma yana maraba da dukkan waɗanda ke muradin daidaita sahu a wannan tafiya daya sanya a gaba na samar da haɗaɗɗiyar Turai.

Shugaban Majalisar Tarayyar Turai Jerzy Buzek yace, Barroso yana sane da abunda ake tsammani daga ɓangarensa, domin haka suna fatan aiki tare dashi cikin shekaru biyar da zai cigaba da jagorantar hukumar gudanarwan turan.

Jose Manuel Barroso nach Wiederwahl
Jawabin Barroso a majalisaHoto: AP

A ɓangarensa Priministan Sweden wanda ƙasarsa ce take rike da zagayen shugabancin EU, cewa yayi goyon bayan da aka bawa Barroso wajen sake zaɓensa babban abun farin ciki ne a gareshi. Yace hakan zai basu damar ɗorewar cigaban da ake bukata , na kalubalantar muhimman batutuwa da suka hada da matsalolin tattalin arziki da sauyin yanayi.

Mai shekaru 53 da haihuwa, Jose Manuel Barroso baiyi shakkan samun goyon baya daga 'yan siyasa masu ra'ayin 'yan mazan jiya ba,amma ɓangaren masu sassaucin ra'ayi , waɗanda sune masu rinjaye na biyu a majalisar Turan, sunki mara masa baya.

Mawallafiyya: Zainab Mohammed

Edita: Ahmad Tijani Lawal