1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin ramuwar gayya a Afirika ta Kudu.

Kungiyoyin matasa a Najeriya sun kai hare-hare a kan kamfanoni 'yan Afirka ta Kudu a Najeriya a matsayin ramuwar gayya ga hare-haren da ake kai wa 'yan Najeriya da ke zaune a Afirka ta Kudun.

Hare-haren nuna kyama da suka faru a kasar Afirika ta Kudu a wannan karon sun yi wa jama'a da dama zafi a  Najeriya duk kuwa da matakan da mahukuntan kasar suka dauka na bayyana cewar suna tuntubar juna a mataki na diplomasiyya.Sanin cewa ba wannan ne karon farko da wannan ta taba faruwa. 

Matasan dai na masu nuna gazawar daukar matakai daga banagaren gwamnatin Najeriyar amma minsitar kasa a ma'aikatar kula da harkokin kasashen wajen Najeriyar Sanata Hon Khadija Bukar Abba Ibrahim ta ce suna daukan mataki a kan lamarin.A yayin da ‘yan sandan Najeriya suka gargadi duk masu kai hare-haren ramuwar a Najeriyar,matasan tuni suka yi kawanya a gaban ginin MTN da ma sauran kamfanonin da suke mallakar kasar Afirika ta Kudu a yanayi na jiran kadan,ya zuwa yanzu dai ana sa ido don ganin mataki na gaba da gwamnatin Najeriyar za ta dauka a kan wannan lamari.

 

Sauti da bidiyo akan labarin