Martanin Nigeria dangane da yan kasar Sin da aka sace a Rivers | Labarai | DW | 06.01.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martanin Nigeria dangane da yan kasar Sin da aka sace a Rivers

Hukumomi a tarayyar Nigeria sun bayyana manufarsu na tuntuban wadanda suka sace maaikatan sadarwa na kasar Sin guda biyar , domin sakin su a yankin Niger Delta.Tun a jiya da safiya nedai dwasu wadanda har yanzu baa san kosu wanene ba suka sace Sinawan guda biyar, a jihar Rivers dake yankin Niger Delta mai albarkatun mai,kuma tuni hukumomin kasar ta Sin suka mika kokensu wa gwamnatin tarayyar ta Nigeria.Kakakin fadar gwamnatin Jihar Rivers Emmanuel Okar ya sanar dacewa jamiai yansanda da hadin gwiwar gwamnati na kokarin gano wadanda keda alhakin wannan taasar,da nu8fin sasanta yiwuwar sakinsu ba tare da wata matsala ba.Ya kara da dacewa gwamnati bazata biya wasu kudaden diyya domin sakin wadanda aka sacen ba.