1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin kungiyar Tarayyar Turai ga bikin zagayowar ranar 11 ga watan Satumba.

September 11, 2006

Yau shekaru biyar cif da aukuwar harin taáddanci na ranar 11 ga watan Satumba da aka kai biranen New York da Washington a Amurka

https://p.dw.com/p/BtyH
Cibiyar ciniki ta duniya (WTO) a lokacin harin 11 ga watan Satumba, hijira, 2001
Cibiyar ciniki ta duniya (WTO) a lokacin harin 11 ga watan Satumba, hijira, 2001Hoto: AP

A jawabin sa ga alúmar Amurka a yayin bikin cika shekaru biyar da harin 11 ga watan Satumba, shugaba George W Bush yace na ci alwashin ba zan manta da darussan wannan rana ba, domin mun kashe lokaci mai yawa muna kallo tare da taájibin wannan mungunyar al´amari wanda ya auku a wannan ƙasaitaccen wuri, kuma hakan ya tunasar da ni cewa har yanzu akwai wani maƙiyi wanda ke da aniyar aikata makamancin wannan ɗanyen aikin da zai yi mummunan illa ga alúma.

Su ma ƙasashen tarayyar turai sun yi jimami tare da ban girma ga waɗanda suka rasu a harin na 11 ga watan Satumba da aka kaiwa ƙasar Amurka, a waje guda kuma suna masu tambaya ga matakan da suka biyo baya wadanda Amurka ke jagoranta na yaƙi da ayyukan taáddanci.

A wata sanarwa da ƙungiyar tarayyar turan ta fitar daga Hedikwatar ta dake ƙasar Finland, wadda a yanzu take riƙe da shugabancin ƙarba ƙarba na ƙungiyar, ƙungiyar ta EU, ta nuna tausayawa ga iyalai da Aminan waɗanda suka rasa rayukan su, tare da nanata yin Allah wadai da ayyukan taáddanci ta kowace fuska.

ƙungiyar tarayyar turan ta ce irin wannan mummunan hari, babu ko shakka ya nuna a fili haɗarin da taáddanci ke da shi ga ɗaukacin ƙasashe na duniya da kuma alúmomin dake cikin ta. ƙungiyar tarayyar turan wadda ke da wakilan ƙasashe 25 na nahiyar turai, ta baiyana yaƙi da taáddanci a matsayin muhimmin abin da ta sanya a gaba, ta kuma baiyana cewa matakan da a yanzu ake ɗauka na yaƙi da ayyukan taáddanci basu wadatar ba, akwai buƙatar ɗaukar ƙarin wasu ƙwararan matakai domin samun cikakkiyar nasara ta ganin cewa yan taádda haƙan su bai cimma ruwa ba.

Sanarwar ta ƙara da cewa zaá cimma nasarar yaƙi da taáddanci ne kawai idan aka sami nasarar aiwatar da matakan yaƙi da ayyukan tarzoman bai ɗaya, aka kuma ɗore a kan haka, sannan da kuma da yin maganin abubuwan dake haddasa yaduwar taáddancin tun daga tushe.

ƙungiyar tarayyar turan ta ce ko da yake tana mai goyon bayan haɗin gwiwa da Amurka domin yaƙi da ayyukan taáddanci, ta ce dukkan matakan da zaá ɗauka na yaƙi da taáddanci, wajibi ne su kasance bisa tsarin doka musamman ma kuma dokar ƙasa da ƙasa.

Gwamnatocin ƙasashen turai da ƙungiyoyin kare haƙƙin bil Adama, sun sha yin kakkausar suka ga wasu manufofin da Amurka ke ɗauka na yaƙi da taddanci musamman yanayin da mutanen da Amurka ke tsare da su bisa ayyukan taáddanci suke fuskanta a sansanin soji na Guantanamo dake Cuba, a waje guda kuma da gidajen kurkuku na sirri da hukumar leƙen asiri ta CIA ke gudanarwa a wasu ƙasashe na ƙetare.

Shugabanin ƙasashen Asia dana ƙungiyar tarayyar turai waɗanda a yanzu haka suke gudanar da taro a birnin Helsinki sun yi tsaiko na miniti guda da misalin karfe goma da rabi na safe domin ban girma ga ɗaukacin mutanen da suka rasa rayukan su a harin na 11 ga watan Satumba, hijira ta 2001.