Martanin Khameini game da zaɓen Iran | Siyasa | DW | 19.06.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin Khameini game da zaɓen Iran

Shugaban addinin ƙasar Iran Ayatollah Ali Khameini yayi kira da a kawo ƙarshen zanga-zangar da ake yi a faɗin ƙasar game da zaɓen shugaban ƙasar da aka gudanar a ranar Juma´a da ta wuce.

default

Shugaban addinin Iran Ayatollah Ali Khamenei

Yayin da yake mayar da martani karon farko a bayyanar jama´a game da jerin zanga-zangar da ake yi na adawa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasar, Ayotallah Ali Khameini yayi watsi da zargin tabƙa wani babban maguɗin zaɓe, inda ya yi gargaɗin cewa ´yan takarar da suka sha kaye ke da laifin duk wani sabon tashen hankali da ka iya faruwa.

A cikin huɗubarsa a babban masallacin Juma´ar birnin Teheran wanda aka watsa kai tsaye ta gidan telebijin, shugaban na addinin Iran ya ce al´umar ne suka zaɓi wanda suke so.

Khameini ya jaddada cewa duk da ƙararraki 646 da ´yan takara uku da suka sha kaye suka shigar game da maguɗin zaɓen a gaban hukumar zaɓe ta majalisar kare juyin juya halin Islama, amma ko shakka babu Ahmedinejad ya lashe wannan zaɓe don ci-gaba da sabon wa´adin mulki na shekaru huɗu musamman dangane da gagarumin rinjayen da ya samu. Ya ce tsarin shari´ar ƙasar ba ya ba da damar yin maguɗi saboda haka ba zai taɓa yiwuwa a yi aringizon ƙuri´u na kimanin miliyan 11 ba. Shugaban na addinin ƙasar yayi kira da a kawo ƙarshen zanga-zangar yana mai kashedin cewa in ba haka ba akwai barazanar fuskantar ƙarin zubar da jini fiye da na rayuka bakwai da suka salwanta. Yayi kira ga shugabannin adawa dake da angizo akan magoya bayansu da su yi takatsantsan game da halayyarsu ta yin kunnen ƙashi.

Kakakin majalisar kare mulkin Islama Abbas Ali Kadkhodaei ya ce za´a gudanar da binciken ƙararraki tsakanin da Allah sannan sai yayi bayani yana mai cewa.

"Zamu yi zama sau biyu domin duba ƙararrakin da aka shigar game da aringizon ƙuri´u. A gobe Asabar ´ya´yan wannan majalisa za su sake zama kuma za su ba da sakamako na ƙarshe bayan wannan zama."

A gobe asabar ´yan adawa na shirin gudanar da sabon taron gangami a birnin Teheran a gobe, inda babban mai ƙalubalantar shugaba Ahmedinejad wato Mir Hussein Mousavi mai matsakaicin ra´ayi zai yiwa jawabi. To sai dai kawo yanzu ƙungiyar da ke goyon bayan ɗan neman canji wadda ta shirya wannan gangami ba ta tabbatar ba ko za ta ci-gaba da gudanar da zanga-zangar kamar yadda ta shirya.

A cikin huɗuɓarsa Khameini ya sake zargin ƙasashen yamma da tsoma baki a harkokin cikin gidan Iran inda ya fito ƙarara ya yi tir da ƙasar Birtaniya yana mai cewa ta fito da maitarta fili.

Mawallafi: Mohammad Nasiru Awal

Edita: Yahouza Sadisou Madobi