Martanin Kasashe kan Taron Annapolis | Zamantakewa | DW | 28.11.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Zamantakewa

Martanin Kasashe kan Taron Annapolis

Kasashen Duniya na cigaba da tofa albarkacin bakinsu

default

George W Bush

Shugaban ƙasar Amurka Geroge W.Bush ya jadada kudirin sa na ganin an kai ga samun wanzuwar zaman lafiya mai dorewa tsakanin Falasdinawa da Israila, jim kadan bayan ganawa ta tsakanin shugaban Falasdinawa Mahmoud Abbas dakuma Firamnistan Israila Ehud Olmert a yayin taron wanzar da zaman lafiya na birnin Annapolis.

Yanzu dai ta tabbata cewar bayan taron na Annapolis, taro na gaba dangane da wanzuwar zaman lafiya a gabas ta tsakiya zai gudana ne a birnin Moscow na kasar Rasha cikin watan janairu na shekara mai zuwa, kuma a lokacin ne ake kyautata zato cewar kasashen Syria da Lebanon zasu tura wakilen su zuwa taron. To amma kafin wannan lokaci ana sa ran bangarorin biyu, zasuyi wata ganawa tare da juna a cikin watan Dizamba mai zuwa.

Du da kasancewar taron sasantawar ya gudana batare da samun halartar wakilen ƙungiyar Hamas ba, to amma kasashen duniya kamar su Birtaniya, da Rasha dakuma Jamus sun bayyana gamsuwa kan manufofin da taron sasantawar na birnin Annapolis zasu haifar wajen shawo kan rikicin gabas ta tsakiya.

Birtaniya tace yanzu kan an ɗauko hanyar samun zaman lafiya mai ɗorewa a gabas ta tsakiya, tun bayan shekaru da dama da ake zaman doya da manja tsakanin falasadinawa da Israila.

Ita kuwa Rasha an saurara ta bakin wakilin ta a taron na birnin Annapolis, kuma ministan harkokin wajen kasar Sergei Lavrov, yana mai bayyana imani kan cewar akwai alamun samun zaman lafiya a gabas ta tsakiya kafin shugaban Amurka ya kammala wa’adin mulkin sa cikin watan janairu na shekara ta 2009.

A bangare guda kuwa ƙasar Jamus ta waiwaya ne baya inda ta duba tarihi dake akwai kan cewar Jamus na da haƙƙi wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a yankin gabas ta tsakiya, mussaman kan Israila, don wannan dalili ne shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel, ta gargadi ƙasar Iran cewar kada ta maido da hanun agogo baya a wannan azama, kana ta gargadi hukumomin Iran dangane da barazanar kai wa kasar Israila hari.

Shugabar tace da shike duniya ta yi Allah wadai da batun nukiliyar kasar Iran, yakamata hukumomin a Tehran su bada hadin kai wajen dakata wa da shirin su na mallakar sinadaren nukiliyar.

A tasa kusurwa ministan harkokin wajen Jamus, Frank-Walter Steinmier, yace kodashike an dauko hanyar warware wannan rikici na gabas ta tsakiya, to amma kada ayi watsi da wannan himma ta sasantawa koda kuwa bayan taron na Annapolis.

Kawo yanzu dai masharhanta game da al’amuran gabas ta tsakiya sun soma hasashe da cewar taron zaman lafiyan yakamata da an gaiyyaci Hamas zuwa taron ganin cewar Mahmoud Abbas na da karfi ne a gaɓar yamma yayin da ita kuma Hammas ke da ta cewa a zirin Gaza. Don haka kenan muddin in ba’a sami goyon baya daga ɓangarorin falasɗinawan biyu ba, to da wuya a yanke hukuncin samun nassara kai tsaye ga batun zaman lafiyar kai tsaye a yankin gabas ta tsakiya.