Martanin Jamus dangane da zaɓen Iran | Siyasa | DW | 22.06.2009
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin Jamus dangane da zaɓen Iran

Gwamnatin tarayyar Jamus ta bi sahu sauran ƙasashen yamma wajen yin kira ga Iran da ta girmama buƙatun jama´a.

default

Aƙalla mutane 10 suka rasu sakamakon arangamar da aka yi ranar Asabar a Teheran babban birnin ƙasar Iran. Wannan al´amarin ya sha kakkausar suka daga ƙasashen yamma waɗanda suka nuna damuwa game da halin da ake ciki a Iran. Ita ma gwamnatin tarayyar Jamus ta tofa albarkacin bakinta dangane da abubuwan da ke wakana a ƙasar ta Iran.

Ba tare da wata rufa-rufa ba shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta ce ta ɗora alhakin abubuwan da suka wakana ƙarshen mako a Teheran babban birnin Iran akan gwamnatin ƙasar, tana mai cewa dole ne Iran ta mutunta ´yancin Bil Adama a matakan da take ɗauka kan masu zanga-zanga.

Ta ce: "A saboda haka ina kira ga shugabannin siyasar Iran da su ba da izinin gudanar da zanga-zangar lumana, su sakarwa kafofin yaɗa labaru mara, kana su daina amfani da ƙarfi akan masu zanga-zanga kana kuma su saki dukkan mutanen da aka tsare."

Hakazalika shugabar gwamnatin ta Jamus ta yi kira da a sake ƙidayar ƙuri´un kamar yadda shi ma ministan harkokin wajen Jamus Frank-Walter Steinmeier da takwarorinsa na Turai suka yi. To sai dai shugabanni a Teheran sun mayar da martani a fusace. Tsohon wakilin Iran a shirinta na nukiliya kuma shugaban majalisar dokoki a yanzu Ali Larijani ya kwatanta kalaman na shugannin Turai da cewa abin kunya ne. Ya ce idan gwamnatocin ƙasashen yamma suka tsoma baki a harkokin cikin gidanta, to Iran za ta sake tunani a dangantakarta da ƙasashen Jamus, Faransa da kuma Birtaniya. To sai dai kakakin gwamnatin Jamus Ulrich Wilhelm ya nuna rashin amincewa da haka.

Ya ce: "Tuni dukkan mu muka yi kira da kiyaye dokokin ƙasa da ƙasa. Ina wa Iran tuni cewa ita tana cikin ƙasashen da suka sanya hannu kan ƙudurin ƙasa da ƙasa gamne da ´yancin jama´a da kuma na siyasa. Saboda haka gwamnatin tarayya ke kira ga Iran da ta girmama wannan ƙuduri musamman na haƙƙin bil Adama da ´yancin furta albarkacin baki da na addini."

A yau Litinin ma´aikatar harkokin wajen Jamus ta gaiyaci jakadan Iran zuwa wata tattaunawa don yi mata bayani game da furucin Larijani. Ko da yake kakakin gwamnatin bai ce uffan ba game da matakan da za a ɗauka a diplomasiyance amma ya ce gwamnatin Jamus na kira ga gwamnatin Iran da ta ba da haɗin kai. Kuma ta na bin manufofi daidai da na taƙaddamar shirin nukiliyar Iran.

Ya ce: "Muna duba dukkan fuskokin guda biyu inda a ɓangare ɗaya muke nuna musu a fili cewa dole su yi aiki da dokokin gamaiyar ƙasa da ƙasa sannan a ɗaya ɓangaren idan suka girmama dokokin kuma suka bayyana haka a fili to za´a ƙarfafa haɗin kai tsakani."

To sai dai a yau Litinin ma an jiyo kalamai masu tsaurai daga birnin Teheran, inda aka rawaito wani kakakin ma´aikatar harkokin waje ya na cewa ba´a kawad da yiwuwar korar wasu jami´an diplomasiyar ƙasashen yamma daga Iran ba.

Mawallafa: Mathias Bölinger / Mohammad Nasiru Awal

Edita: Umaru Aliyu