Martanin Jamus dangane da sabuwar gwamnati a Zimbabwe | Siyasa | DW | 16.09.2008
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin Jamus dangane da sabuwar gwamnati a Zimbabwe

Jamus dai ta yi takatsantsan wajen mayar da martani ga yarjejeniyar raba madafun iko a Zimbabwe.

default

Firaminista Tsvangirai da shugaba Mugabe da kuma mataimakin firaminista Mutambara, a birnin Harare

Jam´iyar shugaba Robert Mugabe ba ta da rinjaye a cikin sabuwar gwamnatin Zimbabwe, sakamakon yarjejeniyar raba madafun iko da ta cimma da ´yan adawa. A Berlin gwamnati ta yi takatsantsan game da martanin da ta mayar kan wannan ci-gaba da aka samu a Zimbabwe.


Gwamnatin tarayyar Jamus ta ƙi ta ce uffan, inda ta bari ƙungiyar tarayyar Turai ta ari bakinta ta ci mata albasa na yin maraba da shigar da ´yan adawa a cikin gwamnatin Zimbabwe sannan ta yi alƙawarin ba da taimako.


Ta haka ba za´a ci-gaba da shirin faɗaɗa takunkumi kan Zimbabwe ba. Maimakon haka a cikin wata sanarwa da ta bayar ƙungiyar EU a Brussels ta ce za ta jira ta ga ko yarjejeniyar za ta ɗore kuma ko gwamnatin riƙon ƙwaryar za ta yi aiki da dokokin demoƙuraɗiyya da mulki na bin doka.


Su ma ´ya´yan majalisar dokokin Jamus sun nuna shakku ga wannan yarjejeniyar. Mai magana da yawun jam´iyar The Greens akan manufofin ketare Kerstin Müller tuni ta yi cewa a Mugabe ya sha kaye a zaɓen a saboda haka wannan yarjejeniyar ba ta dace da buƙatun al´umar ƙasar ba.

A nata ɓangaren masaniyar harkokin siyasar Afirka ta jam´iyar FDP Marina Schuster ta goyi da bayan ƙara matsawa shugaba Mugabe lamba ne.

Ta ce: "Ko shakka babu raba madafun ikon shi ne zaɓi guda ɗaya bayan murɗiyyar zaɓen. Amma ayar tambaya a nan ita ce yaya sabuwar gwamnati da shi kan shi firaminista Changirai za su tinkari matsaloli iri daban daban da suka yiwa ƙasar katutu. Wace irin rawa firaministan zai taka kuma wane irin haɗin kai za a samu tsakanin sabbin hukumomin gwamnati?"

In ban da taimakon jin ƙai da tallafawa ƙungiyoyin masu zaman kansu dake aiki a Zimbabwe da ma´aikatar haɗin kan tattalin arzikin Jamus ke bayarwa, tun bayan zaɓen shekara ta 2002 wanda shi ma aka tursasawa ´yan adawa, Jamus ɗin ta daina bawa Zimbabwe taimakon raya ƙasa kai tsaye. Shin ya kamata a ɗage wannan takunkumi don taimakawa wannan ƙasa da talauci ya yiwa katutu ta sake tsayawa kan ƙafafunta. Marina Schuster ta nuna shakku.

Ta ce: "Ina ganin ba wani dalilin yin ɗoki. Dole mu sa ido mu ga yadda abubuwa za su kasance. Bai kamata mu yi riga malam masallaci ba, domin duk wani taimakon tattalin arziki da za mu bayar yanzu zai faɗa hannun gwamnati ne yayin da talakawa za su ci-gaba da zama cikin mummunan talauci."

To amma wasu ´yan siyasa sun roƙo da sake komawa ga taimakon raya ƙasa sannan a gindayawa jam´iyar ZANU-PF sharaɗi kafin a ɗagewa Zimbabwe takunkumin.