Martanin jam′iyyun siyasa game da zaɓukan jihohin Berlin da Mecklenburg-Vorpommern da aka gudanar a nan Jamus. | Siyasa | DW | 18.09.2006
 1. Inhalt
 2. Navigation
 3. Weitere Inhalte
 4. Metanavigation
 5. Suche
 6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin jam'iyyun siyasa game da zaɓukan jihohin Berlin da Mecklenburg-Vorpommern da aka gudanar a nan Jamus.

A jiya lahadi ran 17 ga watan Satumba ne aka gudanad da zaɓen majalisun jihohin Berlin da Mecklenburg-Vorpommern a nan Jamus, inda sakamakon da aka bayar ke nuna cewa Jam'iyyar SPD ce ta fi samun rinjayi. Duk da hakan dai sauran jam'iyyun ma sun yabi irin sakamakon da suka samu.

Kurt Beck, shugaban jam'iyyar SPD.

Kurt Beck, shugaban jam'iyyar SPD.

Ra’ayoyi dai sun bambanta kan nasarorin da jam’iyyar SPD ke kambama kanta da cewa ta samu, a zaɓukan jihohin Berlin da na Mecklenburg-Vorpommern, da aka gudanar jiya a nan Jamus. A duk majalisun biyu dai, jam’iyyar SPD ce ta fi samin rinjayi. Amma duk da haka, wasu masharhanta na ganin cewa, Firamiyan jihar Mecklenburg-Vorpommern, Harald Ringsdorf na jam’iyyar SPD ne ya sha kaye, saboda jam’iyyarsa ta yi asarar kusan kashi 10 cikin ɗari na ƙuri’un da aka ka da. Sai dai wannan ra’ayin, bai hana shugaban jam’iyyar SPD ɗin, Kurt Beck, bayyana farin cikinsa game da sakamakon da ta samu a zaɓen gaba ɗaya ba:-

„Da farko ina taya Klaus Wowereit da Harald Ringstorff murna, saboda nasarar da suka samu a jihohinsu, inda kuma za su zarce da mulki. Dukkanmu dai burinmu ke nan a yaƙin neman zaɓe. Mun kuma cim ma wannan burin. Ina matuƙar farin cikin ganin cewa, masu zaɓe a birnin Berlin, sun tabbatar wa Klaus Wowereit ci gaba da muƙaminsa. Jam’iyyar Social Democrats a nan Berlin dai ta ƙara samun nasara, abin da ke nuna cewa, mazauna birnin na sha’awar ganin Klaus Wowereit ya ci gaba da aikinsa na magajin birni.“

A duk jihohin biyu dai, jam’iyyar CDU ta sha kaye. Amma kamar yadda sakatare-janar na jam’iyyar Ronald Pofalla ya bayyanar, jam’iyyarsa na da isassun ƙuri’u na janyo sauyin mulki a jihar Mecklenburg-Vorpommern.

Duk masharhanta dai sun yarje kan cewa, jam’iyyun gurguzu na PDS da WASG ne suka fi shan kaye a zaɓukan. A Berlin, jam’iyyar PDS ta yi asarar kusan kashi 10 cikin ɗari, idan aka kwatanta sakamakon da ta samu a wannan karon da na zaɓen shekaru 4 da suka wuce.

Jam’iyyar Greens ma ba ta ci nasarar shiga majalaisar Mecklemburg-Vorpommern ba. Sakamakonsu ya zo daidai da na jam’iyyun gurguzu. Shugaban jam’iyyar Claudia Roth ta ce a nata ganin dai sakamamkon na nuna farfaɗowar jam’iyyar, wadda a shekarun baya ta yi ta shan kaye a zaɓukan jihohin tarayya:-

„Ai mun sami kyakyawan sakamako. A Berlin ma zan iya cewa, jam’iyyar Greens ce ta fi samun nasara. Idan aka bi diddigin lamarin, za a ga cewa sauran jam’iyyun duk a bayanmu suke. Jam’iyyar PDS kuwa, ita ce ma baya-baya, a can ƙarshe. Kowa dai ya ga irin sakamakon da aka samu. A nawa ganin, mazauna birnin Berlin sun zaɓi jam’iyyun haɗin gambiza na SPD da Greens ne, amma tare da ba da muhimmanci ga jam’iyyar Greens.“

Shi ma shugaban jam’iyyar FDP mai bin sassaucin ra’ayi, Guido Westerwelle, ya yabi sakamakon da jam’iyyarsa ta samu a zaɓukan:-

„A Berlin mun sami kyakyawan sakamako, wanda shi ne a jeri na biyu mafi inganci, tun haɗewar Jamus. A Mecklenburg-Vorpommern ma, mun sami gagarumar nasara. Abin farin ciki ne ganin yadda muka ci nasara a jihar, musamman idan aka yi la’akari da cewa, a shekaru 12 da suka wuce, ko shiga zaɓe a jihar ma bam u yi ba.“

Duk da wannan kambama kanta da jam’iyyar FDP ke yi, ba ta da isassun ƙuri’u na samun damar shiga wata gwamnati a jihar. Su ko jam’iyyun ’yan tsageru kamarsu Republikaner da NPD, dukkansu ba su sami shiga cikin majalisar birnin Berlin ba. A majalisar Mecklenburg-Vorpommern ne jam’iyyar NPD ta sami wakilci, amma wanda ba shi da wani muhimmancin da sai an dama da ita kafin a zartad da ƙudurori.

 • Kwanan wata 18.09.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bty6
 • Kwanan wata 18.09.2006
 • Mawallafi YAHAYA AHMED
 • Bugawa Buga wannan shafi
 • Permalink http://p.dw.com/p/Bty6