Martanin Jami′iyyun Jamus dangane da zaɓen ′yan majalisar jihar NRW | Siyasa | DW | 10.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Siyasa

Martanin Jami'iyyun Jamus dangane da zaɓen 'yan majalisar jihar NRW

Jami'iyyun haɗakar Jamus sun kaɗu dangane da sakamakon zaɓen Nordrhein-Westfalen da suka sha kaye

default

Hannelore Kraft

Jami'iyyar shugabar gwamnatin Jamus ta Christian Demokrates da abokan haɗakarta na Free Demokrats dai sun yi asarar  rinjaye a majalisar Dottijan ƙasar, sakamakon kayen da suka sha a zaɓukan 'yan majalisar dokoki na jiha mai mafi yawan al'umma jamus ta Nordrhein Westphalia daya gudana a jiya Lahadi.

Ita kanta Jami'iyyar SPD data tayi nasarar lashe zaɓukan ta kasa ɓoye mamaki, musamman bisa la'akari da irin kaye data sha fuskanta a zaɓukan baya. A dangane da wannan nasara ce aka gudanar da liyafa ta murna a headquatar jami'iyyar dake Willy-Brandt- Haus a birnin Berlin, bukin daya samu halartar shugaban SPD na ƙasa Sigmar Gabriel....

" wannan abu ne da wannan gida ya daɗe bai gani ba balle ji. Lokaci ne na murna da farin ciki kamar yadda muke ciki a wannan yammaci".

A bayanan Gabriel ba wai masu  kaɗa kuri'un dai ba wai sun zaɓi jami'iyyar SPD ne da babbar 'yar takararsu ba, amma har da nuna rashin amincewa da jami'iyyar haɗaka dake jagorantar mulkin Jamus a halin yanzu....

Claudia Roth Bundesvorsitzende BÜNDNIS 90/DIE GRÜNEN

Claudia Roth

" Babu shakka  mutanen da kansu sun bayyana,domin nuna alamar kawo ƙarshen abunda  aka tsara aiwatarwa cikin 'yan watanni da suka gabata, wanda bawai kawai matsaloli bane, amma har da salon siyasar da ta shafi mutanen, abunda Merkel da Westerwelle ke neman aiwatarwa da suka shafi haraji wa birane da yankuna da komar da batun sake inganta harkokin samarda makamashi"

Ita ma jami'iyyar kare muhalli ta the Greens, sakamakon zaɓen na Nordrhein Westphalia a babban abun murna ne a ɓangarenta, kasancewar  ta samu gagarumar nasara. Wannan sakamakon nada matukar muhimmanci a siyasa Jamus a matakin tarayya a cewar shugabar jam'iyyar Claudia Roth..

" Mun cimma gagarumar nasara. Bawai  a jihar Nordrhein Westphalia ne kawai zamu haifar da sauyi a manufofi ba, amma har da Berlin, inda abubuwa ba zasu cigaba da tafiya ba. A majalisar Dottijai akwai wasu masu rinjaye, kuma hakan  wani sakamako ne wa jami'iyyun haɗaka da ke mulki na CDU da FDF, bawai kawai a jihar NRW ba amma har da sama"

Deutschland Bundesregierung Finanzkrise Griechenland Angela Merkel und Guido Westerwelle

 A yanzu haka dai gwamnatin haɗakar ta CDU da FDP ta rasa rinjayen da take dashi a majalisar dottijan na Jamus, wanda hakan ne ya hana jami'iyyar CDU gudanar da wata liyafa a headquatarta da ke Konrad-Adenauer Haus a Berlin.

Bayan kaɗuwa  dangane da wannan kaye a sakamakon zaɓen na jiya dai , babban sakataren jami'iyyar CDU ta ƙasa Hermann Gröhe ya bayyana cewar bawai a jihar NRW ne kaɗai wannan sakamako zai shafa ba, amma har a fuskar tsarin mulkin ƙasa.....

"har da irin zazzafan  kafa tushen haɗakar da aka fuskanta tsakanin CDU da FDP , da cece-kuce da suka mamaye tattaunawar hadakar sun taimaka  kamar yadda muka gani cikin 'yan makonni da suka gabata".

Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Ahmad Tijani Lawal