Martanin Isra´ila ga kalamomin shugaban kasar Iran | Labarai | DW | 27.10.2005
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martanin Isra´ila ga kalamomin shugaban kasar Iran

Mataimakin Praministan Israela Shimon Perez, ya maida martani, ga kalamomin shugaban kasar Iran Mahamud Ahmadi Nejad.

Jiya ne shugaban na Iran, ya gabatar da wani jawabi a taron lacca gaban dalliban kasar, su fiye da dubu 3, inda ya kada baki ya ce, kwata-kwata kamata tayi, a shafe haramtaciyar kasar Israela daga doran kasa.

Bai dace ba,sam inii shi, kasashen larabawa, su amince bani yahudu, tsofin abukan gabar su,su girka kasa, a tsakiyar yankin larabawa.

Mataimakin Praministan Israela, ya rubuta wasika zuwa ga Ariel Sharon , inda ya bukaci cikin gaggawa Israela ta aika bukatar ta ga sakatare Jannar na Majalisar Dinkin Dunia Koffi Annan, da komitin Sulhu, domin a kori Iran, daga sahun kasashe membobin Majalisar Dinkin Dunia.

A cewar Shimon Perez ba ta kamata, a daidai lokacin da a ke neman zamen lahia mai dorewa a dunia, bai dace ba, a daidai wannan lokaci, da ka shiga tantanawa ta zahiri, tsakanin Isrela da Palestinawa, tare da sa hannun kasashe da kungiyoyi na dunia, wani shugaban kasa, ya fito ya na wannan kalamomi na batanci da renin wayo.