Martanin Isra´ila ga harbe-harben rokoki daga Labanon
May 28, 2006Talla
Kasar Isra´ila ta maida martani, ga harbe harben rokokin da wasu mutane daga kasar Labanon su ka yi ga wannan sansanin sojan ta asahiyar yau lahadi.
Hukumomin Isra´ila sun bayyana sanarwar ɗora alhakin harin, ga gwamnatin Labanon.
Kazalika sun ce, za su shigar da kara gaban komitin sulhu na Majalisar Dinkin Dunia.
Wani kakakin jami´an tsaron kasar Labanon, ya sanar cewa harin na Isra´ila, ya yi setinwasu rundunoni, mallakar yan tsatsauran ra´ayin Palestinu, da ke jibge a kasar. Sojoji 6, su ka ji mumunan raunuka, a sakamakon wannan hari.