Martanin Iran kan makamashin Nukiliya. | Labarai | DW | 23.08.2006
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martanin Iran kan makamashin Nukiliya.

Manyan ƙasashe shida masu faɗa aji na duniya na nazarin tayin da Iran ta gabatar na ƙarin tattaunawa domin sulhunta rikicin nukiliyar ta. Iran ɗin dai ta ce amsar da ta bayar, na tayin Ihsanin da manyan ƙasashen suka yi mata, ya ƙunshi managartan shawarwari waɗanda za su bada damar tattaunawa ta hakika domin sulhunta taƙaddamar ba tare da jinkiri ba. A hannu ɗaya dai babu wata alama dake nuni da cewa Iran ta aminta da buƙatar kwamitin tsaro na Majalisar ɗinkin duniya wanda ya umarci ta dakatar da bunƙasa sinadarin Uranium nan da ranar 31 ga wannan watan na Augusta ko kuma ta fuskanci sanya mata takunkumi. Iran ta baiyana waádin da cewa ba shi da maána. Jamiín harkokin wajen ƙungiyar tarayyar turai Javier Solana yace amsar Iran ɗin na buƙatar yin nazari cikin nutsuwa. Ƙasashe biyar masu kujerar dundundun a kwamitin sulhun Majalisar ɗinkin duniyar waɗanda suka haɗa da Britaniya da China da Rasha da Faransa da Amurka da kuma Jamus waɗanda suka gabatar da tayin Ihsanin a game da moriyar da Iran zata amfana da su idan ta dakatar da shirin ta na nukiliyar, basu bayar da martani ba tukuna a hukumance, sai dai kuma Maáikatar harkokin wajen China ta ce, ta yi Imani hanya mafi dacewa ta sulhunta taƙaddamar ita ce ta hanyar diplomasiya.