1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Iran game da takunkumi

June 9, 2010

Iran tace babu wani ta'asirin da takunkumin Majalisar Ɗinkin Duniya zai yi mata

https://p.dw.com/p/NmUi
Hoto: AP

Shugaba Mahmud AhmadineJad na ƙasar Iran ya bayyana sabbin takunkumin da kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince a sanyawa ƙasar da cewar hauragiya ce, kana ɓata lokaci ne kawai kwamitin ya yi. Kamfanin dillancin labaran ƙasar Iran ya ruwaito shugaba AhmadineJad na cewar, matakin bai taka karya ya karya ba, kuma tuni ya aikewa ɗaya daga cikin mambobin kwamitin sulhun saƙon da ke cewar matakin sanya takunkumin tamkar wata tsummar da aka ƙare amfani da ita ne, wadda jefata a kwandon shara ne ya fi dacewa da ita. Shugaban na Iran, wanda a halin yanzu ke yin ziyarar aiki a ƙasar Tajikistan, ya ce babu wani lahanin da ƙasashen yammacin duniya za su iya yiwa ƙasar sa.

Ɗazunnan ne kwamitin sulhun Majalisar Ɗinkin Duniya ya amince da sanyawa Iran zagaye na huɗu na takunkumi bisa shirin niukiliyar ta, wanda ƙasashen yammaci ke zargin na da nufin ƙera makaman ƙare dangi ne. Mammbobi12 daga cikin kwamitin sulhun - mai mambobi 15 ne dai suka yi na'am da ƙudurin, a yayin da ƙasashen Brazil da Turkiyya, waɗanda ke da kujera - amma ba na din din din ba a kwamitin suka jefa ƙuri'ar nuna adawa da matakin.

Mawallafi : Saleh Umar Saleh

Edita : Andullahi Tanko Bala