Martanin Iran a kan makaman Nukiliyan Amurka | Labarai | DW | 04.05.2010
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martanin Iran a kan makaman Nukiliyan Amurka

Amurka ta sanar da mallakar makaman Nukiliya dubu biyar da ɗari ɗaya da goma sha uku

default

Hillary Clinton

Iran ta bayyana mallakar makaman Nukiliya 5,000 a ɓangaren Amurka, a matsayin rashin adalci da barazana ga zaman lafiya a Duniya baki ɗaya. Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Tehran Ramin Mehmanparast ya ce akwai bukatar gudanar da bincike dangane da yawan makaman Nukiliyan Amurkan.  A jiya ne dai a karon farko, Amurkan ta fito fili wajen sanar da cewar tana mallakar makaman Nukiliya kimanin 5,113.  Kazalika kakain na Iran yayi watsi da zargin da sakatariyar harkokin wajen Amurka Hillary Clinton tayi wa Shugaba Ahmadinejad, na adawa da Amurka a taron Majalisar Ɗunkin Duniya na hana yaɗuwar makaman Nukiliya a birnin New York.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Edita: Umaru Aliyu