1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin fadar white House game da yakin Iraqi

September 25, 2006
https://p.dw.com/p/BuiK

Fadar White House ta soki rahoton da wata jarida ta buga wanda ya baiyana nazarin hukumomin leƙen asiri na Amurka, da ya danganta cewa yaƙin da Amurkan ke gudanarwa a Iraqi ya haifar da ƙaruwar ayyukan tarzoma a duniya. Wani mai magana da yawun fadar ta white House yace bayanan da jaridar ta New York Times ta buga bai ƙunshi ɗaukacin abin da rahoton ya kun sa ba. Jaridar ta baiyana cewa binciken da jamiái goma sha shida na hukumomin leƙen asirin Amurka suka gudanar ya tabbatar da cewa tsundumar sojojin Amurka a ƙasar Iraqi ya taimaka wajen assasa wasu ƙungiyoyi masu tsatsauran raáyi mabanbanta da ƙungiyar al-Qaída. Rahoton wanda aka yiwa laƙabi da hasashen bayanan tsaron ƙasa, shi ne nazari na farko wanda hukumomin leƙen asiri na Amurka suka gudanar a hukumance, domin tantance halin da ake ciki game da ayyukan tarzoma a duniya, tun bayan fara yaƙin Iraqi a watan Maris na shekara ta 2003