Martanin EU a game da jawabin Bush dangane da gabas ta tsakiya | Labarai | DW | 17.07.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martanin EU a game da jawabin Bush dangane da gabas ta tsakiya

Komishinan harakokin waje na ƙungiyar gamayya turai Havier Solana, ya bayana matuƙar gamsuwa, a game da hurucin shugaban kasar Amurika Georges Bush a kann rikicin gabas ta tsakiya.

Idan dai ba amanta ba, ranar jiya ne,shugaba Bush ya gabatar da jawabin, wanda a cikin sa ya alƙawarta yin iya ƙoƙarin sa, domin tabbatar da wanzuwar ƙasashe 2 masu maƙwabtaka da juna, wato Isra´ila da Palestinu, tare da kitsa mu´amila ta cuɗe ni in cuɗe ka, a maimakon yaƙar juna, da su ke ci gaba da yi, a halin yanzu.

A cewar Havier Solana wannan shine karo na farko da shugaban Amurika ya ambata yiwuwar kasancewar ƙasashen 2.

A tantanawar da yayi yau, da Tony Blair,saban mai shiga tsakanin rikicin gabas ta tsakiya, Solana ya buƙace shi, da yayi anfani da wannan dama, domin cimma burin da a ka sa gaba.