1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin duniya kan harin Spain

Ramatu Garba Baba MNA
August 18, 2017

Shugabannin kasashen duniya suna mayar da martani a kan harin da aka kai a kasar Spain da ya halaka mutane 14.

https://p.dw.com/p/2iTAa
Nach Terroranschlag in Barcelona
Hoto: picture alliance/AP Photo/M. Fernandez

Firaministar Britaniya Theresa May ta ce ya zama wajibi a hada karfi don yaki da ayyukan ta'addanci, don a gudu tare a tsira tare, a cewar ta duk kasashen duniya ne ke fuskantar wannan annoba ta barazanar ta'addanci. A na shi bangaren Firaminstan kasar Spain Mariano Rajoy ya jadadda bukatar tashin kasashen duniya tsaye don yakar ta'addanci.

Kasar Poland kuwa a ta bakin ministan harkokin cikin gidan kasar Mariusz Blaszczak ta ce duk da cewa Poland ba ta fuskantar barazanar mayakan IS, duk da haka akwai bukatar shugabannin kasashen Turai su matsa kaimi wajen dakile ayyukan ta'addanci a nahiyar.

Rahotanni daga kasar Spain na cewa akwai yiwuwar direban da ya kutsa motar cikin cunkoson jama'a na daga cikin mutane biyar da jami'an tsaron suka halaka a lokacin da suka yi kokarin shawo kan lamarin a ranar Alhamis.

Mamata da kuma wadanda suka sami rauni a harin sun kunshi 'yan kasashe 35 da suka kunshi Jamus da Faransa da Benezuwela da Australiya, da Ireland, sai Peru, da Aljeriya da kuma kasar Chaina.