1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin duniya dangane da hare-hare a Spain

August 18, 2017

Kasashen duniya na ci gaba da sukar harin da aka kai a kasar Spain da ya halaka mutane akalla 14 da raunata wasu masu yawa. Harin na birnin Barcelona ya ritsa da 'yan kasashe da dama.

https://p.dw.com/p/2iTy6
Schweigeminute für die Opfer des Anschlags von Barcelona
Hoto: Ihab Fahmy

Akalla dai 'yan kasar Jamus 13 ke cikin wadanda suka jikkata a harin na Barcelona, haka ita ma kasar Amirka ta sanar da cewa akwai dan kasarta cikin wadanda suka mutu, yayin da suke ci gaba da tantance wadanda suka jikkata, kamar yadda sakataren harkokin wajen Amirka Rex Tillerson ya sanar.

Philippinen Manila - Rex Tillerson
Hoto: picture-alliance /dpa/Reuters Pool/AP/E. De Casto

Yadda Amirka ta ji da harin

 "Ina son tattabar muku cewa, an shaida mana a hukumance, akwai dan Amirka guda da ya mutu a harin ta'addancin Spaniya. Muna ci gaba da tantance ko akwai karin Amirkawa cikin wadanda suka jikkata. Muna mika jaje ga iyalan wadanda suka rasu"

Turkiyya ta ce batun ta'addanci babu bambanci

Shi ma firaministan Turkiyya, Binali Yildirim ya aika sakon ta'asiyar kasar ga gwamnati da al'ummar Spaniya.

"Mun yi Allah wadai da wannan harin ta'addanci, kuma muna taya Spaniyawa alhinin abin da ya faru. Bai kamata mu rika bambanta ta'addancin wata kasa da na wata ba. Kamata ya yi mu sani cewa muna bukatar hada kai a yaki da ta'addanci a duniya baki daya. Ya kamata mu rika musayar bayanai da hada kai wajen kawar da ta'addanci"

Martanin Majalisar Dinkin Duniya

USA UNO Konferenz Libyen
Hoto: Getty Images/A. Burton

A can Majalisar Dinkin Duniya ma kwamitin sulhu ya yi tir da harin na kasar Spain. Kamar yadda jakadan kasar Masar Abdoulatif Aboulatta, kasar da a yanzu ke shugabancin kwamitin sulhu na karba karba ya bayyana.

 "A Madadin mambobin kwamitin sulhu, ina son yin tir da kakkausar murya bisa danyen aiki na ta'addanci a Barcelonan kasar Spaniya. Mambobin majalisar baki daya sun yi Allah wadai da harin, kuma muna jajantawa iyalan wadanda suka mutu da gwamnatin Spaniya"

Rahotanni daga kasar ta Spain na cewa akwai yiwuwar direban da ya kutsa motar cikin cunkoson jama'a na daga cikin mutane biyar da jami'an tsaron suka halaka, a lokacin da suka yi kokarin shawo kan lamarin na jiya Alhamis. Mamata da kuma wadanda suka sami rauni a harin, sun hada da 'yan kasashen Jamus da Faransa da Benizuwela da Australiya da Ireland da Peru da Algeriya da kuma kasar China.