Martanin Britania kan rahotan UNICEF | Labarai | DW | 14.02.2007
  1. Inhalt
  2. Navigation
  3. Weitere Inhalte
  4. Metanavigation
  5. Suche
  6. Choose from 30 Languages

Labarai

Martanin Britania kan rahotan UNICEF

Hukumomin Britania sun yi watsi da rahotan asusun kula da ilimin kananan yara ta UNICEF ,nacewa itace ta karshe a jerin kasashe masu arzikin masaantu 21 da bata bawa yaran kasar kyakkyawar kulawa da suke bukata.Kakakin gwamnatin kasar ya bayyana cewa wanna rahoto na UNICeF ya taallaka ne akan halin da yaran ke ciki a baya amma ba yanzu ba.Ya bada misalin rage daukan ciki a bangaren yara mata da shekarunsu suka gaza 20 da haihuwa..Kasashen Holland da Sweden da denmark da Filland nedai suke a jerin farko na kasashen dake kulawa tare da kyautatawa rayuwar yara,inji wannan rahoto na UNICEF,ayayinda Amurka ce tazo ta 20 kana Britania ta kasance kasa ta 21 kuma ta karshe a jerin kasashe masu cigaban masanaantun.Rohotan kula da ilimin kananan yaran dai yayi laakari ne da halin rayuwar yara da suka halarda iliminsu da lafiyarsu da kariya da dangantaka da kuma halayyarsu da barazanarta garesu.