1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Martanin Amirka kan bayanan WikiLeaks

Salissou BoukariJune 24, 2015

Amirka ta sanar cewa bata sauraron hirarrakin shugaban kasar Faransa na yanzu Francoi Hollande, kuma ba za ta yi hakan ba, kamar yadda ake cece-kuce a kai a halin yanzu.

https://p.dw.com/p/1FmVm
Symbolbild NSA Überwachung
Hoto: imago/Roland Mühlanger

Wannan kalami ya fito ne daga kakakin kwamitin tsaron kasar ta Amirka Ned Price bayan cece-kucen da ya biyo bayan wallafa wasu bayanan da ke cewa, kasar ta Amirka ta yi ta sauraron shugabannin kasar Faransa tun daga Jacques Chirac, zuwa Nicolas Sarkozy da kuma shi François Hollande. Price ya kara da cewa, su na ayyuka hannu da hannu da kasar Faransa bisa dukkan batutuwan da suka shafi tafiyar duniya, kuma kasar Faransa na a matsayin babbar abokiyar huldar Amirka.

Sai dai kuma kasar ta Amirka bata fito ta karyata zargin, ko kuma ta gaskata shi ba. Shafin nan mai kwarmato da bayanan sirri na WikiLeaks ne ya wallafa labarin, kuma shugabansa Julian Assange ya sanar cewa akwai ma wasu labaran tafe nan gaba.